Jihar Kano ce ta uku a jihohin da aka fi amfani da kiran wayar salula, in ji hukumar NBS. Hoto/Getty Images

Hukumar Kididdiga ta Nijeriya, (NBS) ta bayyana jihohin Legas, Ogun da Kano a matsayin wadanda suka fi yawan masu amfani da wayar salula, da kuma masu amfani da intanet.

A wani rahoto da ta saba fitarwa duk bayan watanni uku, NBS ta yi bayani kan harkokin tarho, wanda ya kunshi bayanai na watannin ukun karshe na shekarar 2022.

Bayanan sun hada da na adadin masu kiran waya, da masu amfani da intanet, da kuma yawan masu amfani da kowane kamfanin sadarwar da ke kasar.

A cikin rahoton, a watannin karshen 2022, jimillar mutanen da suka yi kiran wayar salula ta kai 222,571,568. Sai kuma jimillar wadanda suka yi amfani da intanet da ta kai 154,847,901.

Jihohin da ke kan gaba a amfani da salula da data

Jihar Legas da ke kudu masu yammacin kasar ce ke kan gaba a yawan masu amfani da salula, mai biye mata ita ce makwabciyarta jihar Ogun, sai kuma Kano da ke arewa maso yammaci, a mataki na uku bisa bayanan na 2022.

Ta daya: jihar Legas, mai masu kiran waya su 26,460,867; da masu amfani da data su 18,702,394.

Ta biyu: jihar Ogun, mai masu kiran waya su 12,994,352; da masu amfani da data su 9,206,614.

Ta uku: jihar Kano, mai masu kiran waya su 12,373,201; da masu amfani da data su 8,470,131.

Jihohin da ke matakin karshe a amfani da salula da data

Ta ukun karshe: jihar Ekiti, mai masu kiran waya su 2,001,846; da masu amfani da data su 1,474,970.

Ta biyun karshe: jihar Ebonyi, mai masu kiran waya su 1,920,996; da masu amfani da data su 1,264,825.

Ta karshe: jihar Bayelsa, mai masu kiran waya su 1,571,692; da masu amfani da data su 1,101,002.

A bangaren kamfanonin salula da ke Nijeriya, a karshen 2022, kamfanin MTN ne ya fi yawan masu yin kiran salula, wadanda suka kai 89,016,678, da kuam masu amfani da data da suka kai 65,619,610.

TRT Afrika