Gwamnatin Jihar Kaduna a arewa maso yammacin Nijeriya ta saka dokar hana fita ta tsawon sa’a 24 a yankin Sabon Garin Nasarawa-Tirkaniya da ke karamar hukumar Chikun.
Wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Ciki Gida ta jihar ta fitar a ranar Litinin ta ce an dauki matakin saka dokar ne sakamakon karya doka da oda da aka yi da suka jawo kisan wasu mutum biyu a yayin wani rikici.
“An umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da dabbaka dokar hana fitar a yankin, don mayar da al’amura daidai, a yayin da ake ci gaba da bincike.”
Sanarwar ta kuma umarci al’ummar yankin da su tabbatar sun bi dokar sau da kafa wacce ta fara aiki ba tare da bata lokaci ba.
A wata sanarwar ta daban kuma, gwamnatin Jihar Kadunan ta haramta duk wasu harkoki da ke da alaka da rikcin da aka samu a al’ummomin Nasarawa da Sabon Garin Nasarawa na yankin Chikun din.
Tuni aka kama mutum uku da ake zargin su da hannu a kisan mutanen biyu da aka yi sakamakon rikicin da ya barke a wajen.
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta haramta duk wasu harkoki masu alaka da rikicin da ya faru ranar Lahadi da daddare da ya yi sanadin mutwar mutum biyu tare da jikkata mutum shida a Sabon Garin-Tirkaniya da ke karamar hukumar Chikun,” in ji sanarwar.
Tuni aka kai wadanda suka jikkata asibiti don duba lafiyarsu in ji sanarwar.
Ta kara da cewa an dauki matakin ne bayan da aka karbi cikakkun bayanai na tsaro daga wajen sojoji da ‘yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya da kuma ganawar gaggawa da aka yi da shugabannin addini da masu masarautu a Kaduna.
Cikin al’amuran da aka hana gudanarwa din sun hada da Kidan Bishi da Kidan Gala da Farauta.
Kazalika gwamnati ta bayar da umarnin kama duk wani da aka kama da alaka da safarar miyagun kwayoyi a Nasarawa and Sabon Garin Nasarawa.
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar ya yabi jami’an tsaro kan kokarin dakile rikicin da gaggawa tare da yi wa iyalan wadanda suka rasu ta’aziyya, yana mai jaddada cewa za a yi bincike sosai.