Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta ce dakarunta na Operation WHIRL PUNCH sun kashe wani gawurtaccen dan ta’adda mai suna Janari.
Rundunar ta ce ta kashe Janari tare da wasu 'yan ta'adda da dama a ranar Alhamis 18 ga watan Janairun 2024.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin saman kasar Edward Gabkwet ya fitar, Janari da yaransa na daga cikin wadanda suka gudanar da hare-hare da dama da garkuwa da mutane a cikin garin Kaduna da kuma kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
“An bayar da umarnin kai musu farmaki ne bayan an hangi Janari da gungunsa a wani wuri kusa da Katako a Karamar Hukumar Igabi da ke Kaduna,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Haka kuma rundunar sojin ta ce alamu sun nuna cewa a lokacin suna shirin kaddamar da wani hari ne wanda ya jibanci garkuwa da mutane wanda hakan ya ja aka kai musu hari nan take.
“Bayanan sirrin da muka samu sun nuna cewa an kashe Janari da wasu ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane. An kuma gudanar da wasu hare-hare ta sama irin wannan a ranar 20 ga watan Janairun 2024 a kan wasu da aka tabbatar ƴan ta’adda ne a maɓoyarsu da ke Chukuba a Jihar Neja inda aka samu nasara daban-daban,” kamar yadda sanarwar da kara da cewa.