Mutum hudu ne ke kan gaba a zaben fidda gwanin da ake gudanarwa. Hoto/GNA

Jam’iyya mai mulki a Ghana ta New Patriotic Party NPP na gudanar da zaben fitar da gwani a yau Asabar, 4 ga watan Nuwambar 2023 domin zaben wanda zai jagoranci jami’iyyar a takarar shugaban kasa wadda za a yi a shekarar 2024.

Daga cikin wadanda ke kan gaba a takarar akwai mataimakin shugaban kasar Dakta Mahamudu Bawumia da dan majalisa mai wakiltar Assin Central Mista Kennedy Ohene Agyapong.

Haka kuma akwai tsohon Ministan Abinci da Aikin Gona Dr Owusu Afriyie-Akoto da tsohon dan majalisa Mista Francis Addai-Nimoh ne ke neman kujerar shugabancin kasar. Sama da deliget 200,000 ne ake sa ran za su jefa kuri’a a zaben, wanda za a gudanar a rumfunan zabe 275 da ke yankuna 16 na kasar.

Tuni aka soma zaben a wasu rumfunan zaben, kuma tuni ‘yan takarar suka saka hannu kan wata yarjejeniya ta amincewa da sakamakon zaben idan ya fito da kuma amincewa kan ba za su fice daga jam’iyyar ba idan ba su yi nasara ba.

Haka kuma sun amince za su mara wa duk wanda ya samu nasara baya domin tunkarar babban zaben kasar wanda za a gudanar a shekara mai zuwa.

NEWS RELEASE: POLICE STATEMENT ON SECURITY ARRANGEMENT FOR THE NPP PRESIDENTIAL PRIMARIES

Posted by Ghana Police Service on Friday, November 3, 2023

Tuni hukumar ‘yan sandan Ghana ta sanar da cewa ta shirya tsaf domin tabbatar da tsoro a yayin zaben fitar da gwanin inda ta ce ta tura jami’anta a fadin kasar domin samar da tsaro.

Haka kuma ta ce a ranar zaben, jami’an nata wadanda za su samar da tsaro a rumfunan zabe za su saka kaya wadanda ke dauke da kyamara.

TRT Afrika