Jagoran hamayya na Chadi yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa a kotu

Jagoran hamayya na Chadi yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa a kotu

Masra, wanda a baya shi ne firaministan gwamnatin riƙon ƙwaryar Chadi, ya yi zargin cewa an tafka maguɗi a zaɓen.
"Da taimakon lauyoyinmu, mun shigar da buƙatarmu ga Hukumar Zaɓe da ta bayyana gaskiyar abin da ke cikin akwatunan zaɓen," in ji Masra, / Photo: AFP

Jagoran hamayya na Chadi Succes Masra ya shigar da ƙara inda yake ƙalubalantar sakamakon farko na zaɓen Shugaban Ƙasar da aka yi ranar 6 ga watan Mayu.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne hukumar zaɓe ta ƙasar ta ayyana Shugaba Mahamat Idriss Deby a matsayin wanda ya yi nasara da kashi 61.3 cikin 100 na yawan ƙuri'un da aka kaɗa, kamar yadda sakamakon farko ya nuna, yayin da Masra ya zo na biyu da kashi 18.53 na jumullar ƙuri'un.

Sai dai, gabanin sanarwar sakamakon a hukumance, Masra, wanda a baya shi ne firaminista na gwamnatin riƙon ƙwaryar, ya yi ikirrain cewa shi ya yi nasara, yana mai zargin hukumar zaɓen da kitsa maguɗi.

"Da taimakon lauyoyinmu, mun shigar da buƙatarmu ga Hukumar Zaɓe da ta bayyana gaskiyar abin da ke cikin akwatunan zaɓen," in ji Masra, kamar yadda ya wallafa a shafukansa na sada zumunta na Facebook da X ranar Lahadi, yana mai kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankulansu.

Zarge-zargen tafka maguɗei

Ya yaɗa kwafin rasiti da ke nuna cewa an shigar da ƙarar gaban majalisar, wacce wani jigo a jam’iyyar hamayya da ke kusa da Masara ya ce sun haɗa da kwafin sakamako daga mazaɓu, da wasu bayanai da suka ƙunshi alƙaluman da aka tattara da kuma bidiyo da ya nuna zargin da ake na cewa an cika akwatuna da ƙuri’n bogi da sauran maguɗi.

“Mun tattara kowaɗane irin bayanai” a cewar mutumin. Ana ƙara samun tayar da jijiyar wuya a fuskar siyasa a Chadi, wacce ita ce ƙasar farko a Yammaci da Gabashin Afirka da ke ƙoƙarin komawa mulkin dimokraɗiyya daga mulkin soja.

Deby ya ƙwace mulki ne a watan Aprilun 2021 lokacin da ‘yan tawaye suka kashe mahaifinsa da ya jima a kan mulki, wato Idriss Deby.

Aƙalla mutum 10 ne aka kashe, ciki har da ƙananan yara, yayin da gommai kuma suka ji rauni, sakamakon harba bindigogi da aka dinga yi na murna ranar Juma’a bayan bayyana sakamakon zaɓen, kamar yadda ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil Adama ta Amnesty International da kafofin watsa labaran Chadi suka bayyana.

Ma’aikatar lafiyar Chadi ta tabbatar da cewa mutane da dama sun jikkata lokacin murnar samun nasarar Deby, amma ta nemi ‘yan jarida da kada su ɗauki bidiyo ko ba da rahoton marasa lafiyar da ke asibiti, matakin da ƙunyiyar ‘yan jarida ta Chadi ta yi Allah wadai da shi.

TRT Afrika