'Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin mai shekara 72, wanda ya yi fiye da shekara 40 yana sarauta, tare da ɗansa da kuma wani ɗan'uwansa./Hoto:OTHER

'Yan Nijeriya sun yi matuƙar kaɗuwa da samun labarin kisan da 'yan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir na Gatawa Isa Muhammad Bawa, bayan da ya shafe kusan wata guda a hannunsu.

'Yan bindiga sun kashe Sarkin Gobir na Yankin Gatawa, da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto ne duk da cewa an tattara kuɗin fansa da ya kai naira miliyan 60 domin tura musu, kamar yadda iyalansa suka tabbatar wa TRT Afrika Hausa.

Ƙanen sarkin, Ibrahim S. Gobir, wanda kuma shi ne yake tattaunawa da 'yan bindigar domin a sake shi, ya shaida mana cewa 'yan bindigar sun amince ya kai musu naira miliyan 60 tare da babura, kuma shi da kansa ya haɗa kuɗin sannan ya tafi sayen baburan.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin mai shekara 72, wanda ya yi fiye da shekara 40 yana sarauta, tare da ɗansa da kuma wani ɗan'uwansa.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana matuƙar kaɗuwarsa game da kisan da aka yi masa, wanda ya bayyana a matsayin "mummuna kuma wannan dabbancin ba zai wuce ba tare da kakkausan martani ba,” in ji wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar ranar Laraba da daddare.

A makon jiya ne wani bidiyo ya yaɗu kamar wutar daji a shafukan intanet, da ke nuna sarkin da ɗansa a hannun 'yan bindiga yana jawabi da neman ɗaukin gwamnati da al'umma kan a ceto shi daga hannun 'yan bindigar.

Lamarin, wanda ya nuna sarkin "cikin ƙasƙanci", ya yi matuƙar tayar da hankulan 'yan Nijeriya inda aka dinga kiraye-kiraye ga hukumomin tsaro su kai masa ɗauki.

Tuni fitattun 'yan Nijeriya ciki har da manyan 'yan siyasa suka soma miƙa ta'aziyya game da kisan Sarkin Gobir na Gatawa.

Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar kuma ɗan takarar shugaban Nijeriya a 2023 a jam'iyyar adawa ta PDP, wanda ya wallafa saƙon ta'aziyyarsa a shafin X, ya soki gwamnatin Nijeriya kan sakaci wurin kuɓutar da sarkin.

"Babu shakka gazawar gwamnati wajen nuna damuwa ko ɗaukar matakan tsaro masu ƙwari sun taimaka wurin ta'azzarar rashin tsaro a baya bayan nan," in ji Atiku Abubakar.

Ya ƙara da cewa, "Ina miƙa ta'aziyyata fa iyalan marigayin, da ilahirin al'ummar Gobir da gwamnatin jihar Sokoto kan wannan mummunan rashi na Sarkin Gobir Alhaji Isa Bawa."

Shi ma Peter Obi, ɗan takarar shugaban Nijeriya a 2023 a jam'iyyar adawa ta LP, ya bayyana damuwa game da kisan da 'yan bindiga suka yi wa Sarki Bawa, yana mai cewa "wannan lamari ya sake fito da irin ta'azzarar da rashin tsaro ya yi a Nijeriya, inda mutane masu daraja kamar Sarki za su fuskanci irin wannan wulaƙanci."

An ƙi bayar da gawar Sarki Isa Bawa

A gefe guda, Masarautar Sabon Birnin Gobir ta ce 'yan bindiga sun saki Kabiru, wato ɗan marigayi Sarkin Gobir na Gatawa Alhaji Muhammad Bawa Isa wanda aka sace su tare.

Sai dai ta ce sun ƙi bayar da gawar marigayin, lamarin da ya jefa su cikin ƙarin ruɗani.

Tun da farko Ibrahim S Gobir ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa ya samu labarin kisan sarkin ne a yayin da yake ƙoƙarin cika sharuɗɗan fansar ɗan'uwan nasa ne.

"Ni kaɗai ne nake magana da 'yan bindigar nan daga cikin zuri'ar Sarki, kuma uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya da shi. A yanzu na tanadi abubuwan da suka buƙata ina jiran wayarsu don mu ji inda za a kai.

"Ba zan yarda sun kashe ɗan'uwana ba sai idan sun kira ni sun gaya min ko kuma sun haɗa ni da shi mu yi magana kamar yadda suka saba," Ibrahim ya faɗa wa TRT Afrika Hausa a wayar tarho da misalin ƙarfe 3.53 agogon Nijeriya.

TRT Afrika