Tun da fari kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa bashin da ya yi wa NNPCL yana barazana ga tsarinsa na shigo da fetur Nijeriya./Hoto:NNPCL

Kamfanin mai na gwamnatin Nijeriya, Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL) ya amince cewa "masu shigo da fetur" suna binsa "dimbin bashi", wanda ya ce yana barazana ga ɗorewar tsarinsa na shigo da fetur ƙasar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye ya fitar ranar Lahadi, ya ce “ɗimbin bashin ya sanya matsi sosai kan kamfanin kuma yana barazana ga ɗorewar shigo da fetur”.

“Kamar yadda Dokokin Kamfanonin Man Fetur suka tanada, NNPCL zai ci gaba da sadaukawa a kan aikinsa na kasancewa madogara ta ƙarshe game da shigo da fetur, domin tabbatar da yalwar makamashi," in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, "Muna haɗa kai sosai da hukumomin gwamnati da lamarin ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki domin ci gaba da rarraba man fetur a faɗin ƙasar nan."

NNPCL ya fitar da sanarwar ce a daidai lokacin da 'yan Nijeriya suke shafe awanni da dama suna layi a gidajen mai ba tare da samun fetur ba a galibin lokaci sakamakon ƙarancinsa a faɗin ƙasar.

Farashin lita ɗaya ta fetur ya ninka fiye da sau ɗaya tun bayan da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya janye tallafin man fetur a watan Mayu na shekarar 2023 a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki, lamarin da 'yan ƙasar ke gani shi ya haddasa tashin gwauron zabin da kusan komai ya yi a ƙasar.

Yanzu haka dai ana sayar da lita ɗaya ta fetur a kan N700, amma duk da haka ba a samunsa a wannan farashi.

Nijeriya na cikin ƙasashen da suke samar da ɗanyen man fetur a duniya, sai dai ba ta iya tace shi sakamakon rashin aikin duka matatun manta, abin da ake ɗora alhakinsa kan rashawa da cin-hanci.

Sau da dama NNPCL yana cewa za a gyara matatun sannan su ci gaba da aiki, amma shiru kake ji.

TRT Afrika