An kuma gagardi masu shirya manyan taruka da kada su rika yin abubuwan da za su jawo turmutsutsu kamar jefa kudi da kaya cikin dandazon jama’a.Hoto:/OTHER

Bayan jerin turmutsutsun da aka samu a sassan Nijeriya daban-daban wadanda suka jawo asarar rayukan mutum 67 ciki har da yara 35, gwamnatocin jihohi sun fara daukar tsauraran matakai a wuraren da ake tara mutane da dama da kuma wuraren da ake raba kayan tallafi.

An samu turmutsutsu a birnin Ibadan na jihar Oyo da birnin Okija na jihar Anambra da kuma Abuja yayin rabon kayan abinci inda turmutsutsun ya jawo asarar rayuka.

Yara 35 ne suka mutu a Ibadan a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Nijeriya yayin wani turmutsutsu raba kayan abinci a ranar Laraba 18 ga watan Disamba.

Sannan mutum 10 ne suka mutu a Abuja kuma wasu 22 suka mutu a Okija a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya a ranar Asabar, 21 ga watan Disamba yayin wasu tarukan rabon kayan abinci.Wadannan mummunan abubuwa da suka faru suna zuwa a daidai lokacin da mutanen kasar da dama suke cikin matsin rayuwa.

Neman izini

A ranar Lahadi gwamnatin jihar Legas ta sanar cewa daga yanzu masu shirya taruka da zai kunshi fiye da mutum 250 wajibi ne su yi rijista kuma su samu izini daga wata hukuma da ke tabbatar da tsaro a jihar.

“Gwamnatin jihar Legas ta damu sosai da jerin turmutsutsun da aka samu a jihar Oyo da Anambra da kuma Abuja. Duk wani ko wata kungiya da take da shirin raba kayan abinci ko tara mutane da yawa, dole sai ya samu izini daga gwamnatin jihar da kuma hukumar jihar da ke tabbatar tsaro,” kamar yadda Kwamishinan Yada Labarai da Tsare-tsare na jihar Legas Gbenga Omotosho ya bayyana a shafukan sada zumunta.

Mahukunta sun ce za a ci tarar duk wanda ya saba wa wannan ka’idar.

Kazalika a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin an fito da wasu sabbin tsare-tsare ga masu shirya taruka inda aka tanadi na’urorin sanya ido da kyamarori da jirage marasa matuka da sauransu.

Shirin ko-ta-kwana

Wajibi ne taruka da suka kunshi mutum fiye da 300 su tanadi ma’aikatan jinya da kuma tsare-tsaren da tanadin ko-ta-kwana.

Gwamnan jihar Anambra Chukwuma Soludo ya bukaci samar da wani tsari ta yadda za a raba kayan agaji ta yadda mutane ba za su rika taruwa a wuri guda ake raba kayan ba, sannan tsarin ya tanadi mayar da hankali kan mutane masu rauni da kuma amfani da kwararrun jami’ai da suka iya tafiyar da dandanzon jama’a.

“Mun kaddamar da gagarumin bincike dangane da abin da ya jawo wannnan turmutsutsun kuma za mu yi da hukumomi masu ruwa da tsaki don magance sakaci da matsalolin tsare-tsare. Muna bayar da muhimmanci ga lafiya da walwalar mutanenmu musamman yayin bayar da kayan agaji. Ya kamata mu yi aiki tukuru wajen kiyaye faruwar irin haka a nan gaba,” in ji Gwamna Soludo kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X.

Sauran jihohi kamar Abia da Akwa Ibom da Kogi sun umarce masu shirya manyan taruka da su tuntubi ma’aikatar tsaro ta jihar da kuma gwamnatocin kananan hukumomi don bin matakan kariya da kuma bayar da agajin idan bukatar hakan ta taso.

Sannan jihohin sun raba wuraren da za a rika raba kayan tallafin, maimakon tara su a wuri guda inda za a raba su ga kanannan hukumomi da mazabu da rumfunar zabe don kula da dandazon jama’a da kiyaye cunkoson jama’a.

An kuma gagardi masu shirya manyan taruka da kada su rika yin abubuwan da za su jawo turmutsutsu kamar jefa kudi da kaya cikin dandazon jama’a.

TRT Afrika