Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya NIS ta samu nasarar ceto ƙanana yara 21 waɗanda aka yi niyyar safararsu zuwa Jamhuriyar Nijar.
An ceto yaran ne a wani shingen bincike da ke Dunari a Ƙaramar Hukumar Geidam da ke kusa da iyakar Nijeriya da Nijar.
A wata sanarwa da hukumar NIS ɗin reshen Jihar Yobe ta fitar, ta bayyana cewa yaran waɗanda aka ceto a cikin wata bas ƙirar Hiace na tsakanin shekara bakwai ne zuwa sha biyar.
“Motar na ɗauke da yara ƙanana daga garuruwan Labule da Ibeto da ke Ƙaramar Hukumar Magama da ke Jihar Neja, zuwa Maine Soroa da ke Nijar,” in ji sanarwar.
Kamar yadda kwanturola na hukumar ta NIS reshen Jihar Yobe S.S Jega ya bayyana, yaran waɗanda ake zargin an yi niyyar safararsu zuwa Nijar ba su san wurin da za a kai su ba.
Haka kuma ya bayyana cewa yaran ba su da wasu takardu na tafiya ko kuma katin ɗan ƙasa a tattare da su.
Hukumar ta NIS ta ce a za a miƙa yaran ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike a kansu da kuma hukunta masu laifi.
Sanarwar ta bayyana cewa akwai wanda ke yi wa yaran rakiya wato Abubakar Saidu mai shekara 28 wanda malamin Islamiyya ne daga garin Anaba na Ƙaramar Hukumar Magama da ke Jihar Neja wanda a halin yanzu yana tsare a hannun jami’an tsaro.