Rundunar Sojin Mali ta ce tana gudanar da bincike game da zargin da ‘yan awaren azbinawa suke wa sojin ƙasar na kashe fararen hula akalla 24 a farkon wannan mako, a wani bincike da ba kasafai ake yi ba na take hakkin dan Adam tun bayan da sojoji suka karbi mulki a shekarar 2020.
Kungiyar fafutukar 'yantar da Azawad, mai fafutukar neman 'yancin kai na Abzinawa a arewacin kasar, ta zargi sojojin M,ali da sojojin haya na Rasha wato Wagner da tare motocin jigilar farar hula guda biyu da ke kan hanyar zuwa Aljeriya daga Gao a ranar Litinin, inda “suka kashe” akalla mutane 24 daga cikin fasinjojin.
Babban hafsan sojojin Mali ya yi tir da irin yadda ake “ɓata wa sojojin suna” inda ya yi wannan batun ba tare da alaƙanta shi da batun kisan farar hular ba.
Sai dai a ranar Juma’ hukumomin kasar sun sanar da ƙaddamar da bincike kan batun mutuwar fararen hula. Sai dai masu sharhi na ganin cewa ba lallai ne binciken ya ɗora laifin kan sojojin hayar Rasha ba.
“Maƙasudin yin wannan binciken shi ne watsi da zarge-zargen da ake yi wa (sojojin) da Wagner, ba tare da ƙoƙarin gano laifinsu ba.
“Akwai yiwuwar sakamakon binciken zai nuna cewa waɗannan zarge-zargen da ake yi ba na gaskiya bane,” in ji Rida Lyammouri, wanda babban mai sharhi ne a Maroko.
Ƙasar Mali ta shafe fiye da shekara goma tana fama da rikici.