Dandalin Fasahar Kula da Lafiya na Access Pool (HTAP )ya maye gurbin dandalin Covid (C-TAP)/ Hoto: Getty Images

Daga Sylvia Chebet

A yayin da duniya ke farfadowa daga illar annobar Covid-19 da ta janyo asarar kusan rayuka miliyan bakwai, an gano yadda hadin kai ne kadai hanyar da za a bi wajen yakar wannan mummunar annoba.

Fasahar Access Pool (C-TAP) da aka samar bayan barkewar annobar korona a 2020, na da manufar tabbatar da adalci da daidaito wajen samun bayanai da tsarin kula da lafiya ga dukkan kasashe

Baya ga kalubalen da ake fuskanta wajen kafa irin wadannan dandali a lokacin annobar mai muni, C-TAP ya samu lasisi 15 a duniya tun daga bangaren bincike, fasahar gano cututtuka, da allurar riga-kafi.

Bayan tsawon shekaru, Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) na shirin kaddamar da Dandalin Fasahar Kula da Lafiya na HTAP, wanda ya maye gurbin C-TAP.

Dandali mai kyakkyawar makoma

Kwararru na hasashen cewa HTAP zai dora kan kyakkyawan harsashin da C-TAP ya assasa, shigar da sabbin sauye-sauye da ke kara inganta jan hankalin jama'a da tallafa wa bukatunsu yadda ya kamata a fagen neman lafiya.

"Adalci da daidaito wajen samun kayan kula da lafiya na da muhimmanci a bangaren lafiya na duniya," in ji daraktan WHO Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, a yayin da yake kaddamar da HTAP.

Dorawa kan abin da muka koya daga C-TAP, wannan sabon yunkuri ya zama muhimmin matakin kaiwa ga samun kayan kula da lafiya da dama ga kowanne bangaren al'umma, ta hanyar yada bayanan kayayyaki, ilimi da sabbin kirkire-kirkiren kimiyya."

Sauki ga Afirka

Dr Ahmed Ogwell, mataimakin daraktan CDC Afirka, ya yabi wannan dandali da cewa "Ana bukatarsa cikin gaggawa" don cike gibin fasahar da ake da ita a yau.

"Wannan na iya zama mai kawo babba sauyi ga nahiyar Afirka da sauran yankunan da cigaba irin na Yammacin duniya bai kai gare su ba." Ya fada wa TRT Afirka.

Dr Ogwell ya kuma zayyana yadda nahiyar ba ta da hakkin mallakar kayan fasaha a bangaren kula da lafiya, matsalar da ta bayyana karara a lokacin annobar Corona.

Ma'aikacin kamfanin samar da allurar riga-akfin SinoVac a China a 2020 yayin tsaka da aiki. Hoto: AP

Kamar dai manhajar da ta gabace ta, HTAP ma na da manufar zama dandalin fasaha da zai hada kai da mutane don yada muhimman abubuwa, ilimi da bayanai, ta hanyar fasahar kere-kere.

Tun da dai dandalin na aikin sa kai ne, Afirka na iya tsirurutar sa wajen amfani da ci gaban da zarar sun fita.

"Idan HTAP ya yi aiki yadda ya kamata, za a shiga wani zamani na ci gaba a nahiyar, saboda za mu iya mayar d ailimi ya zama asalin hajar da muke bukata don amfani," in ji Dr Ogwell.

Rashin daidaito a cigaban kere-kere

A dai wannan yanayi, ya kuma bayyana rashin tabbas din da ake da shi game da ko wadanda suka mallaki wannan babbar fasaha za su yarda su yi baiwa wasu kasashen.

A lokacin da ake cikin yanayin gaggawa, akwai wasu abubuwan da ya kamata a samu a matakai daban-daban a duniya, da za su saukaka wa wadanda ba su da cigaba a harkokin kula da lafiya," in ji Dr Ogwell. "Abin takaici, wannan bai faru yadda ya kamata ba a lokacin annobar."

Duk da wannan, mataimakin shugaban na CDC Afirka na sa rai da fatan cewa HTAP, duba ga yarjejeniyar da aka tsaya a kai, zai karfafi gwiwar mutane su bayar da gudunmowar ilimi da kwarwarsu ga wannan manhaja ko dandali.

"Ina matukar sa ran cewa dan adam na iya yin komai. Kuma idan muka ce za a iya magance cuta iri kaza d akayan kula da lafiya iri kaza, kuma wani da dabarar yin hakan a hannun sa, to za su yada shi a manhaja ko dandalin HTAP." in ji shi.

A watanni uku na biyun 2024 za a kaddamar da HTAP. Ana dakon hakan kuma, WHO za su nemo damarmakin da za su tabbatar da an fadada fasahar kula da lafiya a dukkan yankunan duniya.

Dr Ogwell ya yi kira ga kasashen Afirka da su kara yawan zuba jari a bangaren kula da lafiya a yayin da suke jiran fitowar wannan cigaba.

"Covid-19 ta koya mana cewa mun yi asara sosai kan gaza cimma manufofin da aka kulla a Abuja," in ji shi, yana mai nuni da cewa za a iya cimma wadannan manufofi.

"Ba zai faru dare daya ba saboda tazarar kudade da bukatar gogayya tsakanin kasashe, amma za a iya cimma wannan buri."

Tare da karin zuba jari, shiri na musamman don ayyukan gaggawa na kula da lafiya, da dama mai fadi ta fasahar kula da lafiya, Afirka na iya kalubalantar matsalolin da take fuskanta a fannin kula da lafiya.

TRT Afrika