Hauhawar farashi a Nijeriya ta karu zuwa kashi 22.04 a watan Maris

Hauhawar farashi a Nijeriya ta karu zuwa kashi 22.04 a watan Maris

Hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS ce ta sanar da batun hauhawar farashin a ranar Asabar.
Babban Bankin Nijeriya dai ya ce yana daukar matakai domin dakile hauhawar farashi a kasar ciki har da kara kudin ruwa. Photo/Getty Images

Hukumar kididdiga ta Nijeriya ta bayyana cewa an samu karuwar hauhawar farashi a kasar a watan Maris daga kashi 21.91 zuwa kashi 22.04 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Fabrairu.

Hukumar ce ta wallafa bayanai game da hauhawar farashin a shafinta na intanet.

Hakan na nufin an samu karuwar hauhawar farashi da kashi 0.13 idan aka kwatanta da makin da aka samu a watan Fabrairu.

Ana kara samun hauhawar farashi a Nijeriya, kasar da ta fi kowace karfin tattalin arziki a Afirka, lamarin da ke kawo cikas ga kudin shiga da jama’a ke samu.

Haka kuma hauhawar farashin ta ja babban bankin kasar ya kara kudin ruwa mafi yawa a kusan shekara ashirin duk da cewa babban bankin ya ce yana daukar irin wadannan matakan ne domin kawo sauki ga hauhawar farashi.

Hauhawar farashin kayayyakin abinci a kasar ta karu zuwa kashi 24.45 daga 24.35 cikin 100 a watan Fabrairu.

Hauhawar farashin kayayyaki da kuma matsin tattalin arziki na daga cikin kalubalen da ke gaban sabuwar gwamnatin kasar. Kasashe da dama dai na fama da hauhawar farashi kuma lamarin ya kara kamari ne tun bayan da aka yi fama da annobar korona.

Sa’annan yakin Ukraine da Rasha na daga cikin abubuwan da masana tattalin arziki suka ce ya kara jefa tattalin arzikin duniya cikin tasku.

TRT Afrika da abokan hulda