Mutane aƙalla 65 waɗanda akasarinsu yara ƙanana ne aka kashe tun daga ranar Asabar a wani harin bama-bamai da Dakarun Rundunar kai ɗaukin Gaggawa ta (RSF) suka kai garin Al Fasher da yankin Darfur a Sudan, a cewar masu fafutuka.
A wata sanarwa da kwamitin 'yan fafutuka na Al Fasher ya fitar a ranar Litinin ya bayyana cewa ''a cikin kwanaki uku kacal, RSF ta kashe yara fiye da 43 da mata 13 da kuma maza tara dukkansu daga cikin al'ummar Al Fasher.''
Sanarwa ta ƙara da cewa "Sama da rokoki 70 ne mayaƙan Janjaweed suka harba a rana ɗaya kacal kan asibitoci da gidaje da masallatai da kuma kasuwanni", tana mai ɗora alhakin lamarin kan dakarun RSF waɗanda suka samo asali daga mayaƙan Janjaweed da suka fara ta'addanci a yankin Darfur tun daga shekarar 2003.
"Yau ya zama ɗaya daga cikin ranaku da aka fi zubar da jinin fararen-hula a Al Fasher a masallatai da asibitoci, musamman ma asibitin Saudiyya," kamar yadda gwamnan lardin Darfur ya rubuta a shafinsa na X.
Da farko dai wani ganau a Asibitin Saudiyya ya bayyana cewa, an kashe mutane 22 a ranar Asabar.
"Shirun da ƙasashen duniya suka yi abin kunya ne," in ji shi.
Miliyoyin mutane sun rasa matsugunansu
Babban birnin arewacin Darfur shi ne birni mafi girma a yankin Yammacin Sudan da har yanzu ba ya ƙarkashin ikon rundunar RSF, wadda dakarunta suka yi wa birnin ƙawanya tun watan Mayu.
Yaƙin Sudan wanda ake fafatawa tsakanin dakarun ƙungiyar RSF ƙarƙashin jagorancin Mohamed Hamdan Daglo da sojojin ƙasar da ke ƙarƙashin Janar Abdel Fattah al Burhan, ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, inda wasu alƙaluma suka nuna cewa adadin ya kai mutum 15,000, a cewar wakilin Amurka Tom Perriello.
Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce Sudan na fuskantar matsalar gudun hijira mafi girma a duniya, inda sama da mutane miliyan bakwai suka yi hijira zuwa wani wuri a cikin ƙasar ko kuma ƙasashen waje saboda yaƙi, sannan sama da mutum miliyan 3.8 ne suka rasa matsugunansu a baya.
Kazalika yaƙin na Sudan ya janyo gargaɗin yunwa, kuma ana zargin ɓangarorin biyu da aikata laifukan yaƙi ciki har da kai wa fararen-hula hari da gangan.
Masu shiga tsakani na Amurka za su sake wani yunƙurin zama a Switzerland a cikin watan gaba mai kamawa domin ganin an kawo ƙarshen faɗan Sudan.
Ana dai sa ran, daga ranar 14 ga watan Agusta ne dai za a buɗe sabon zaman tattaunawar.