ECOWAS ta kara da cewa tana "aiki babu kakkautawa da wadannan kasashe domin ganin an dawo da tsarin mulki."/Hoto:Fadar shugaban Nijeriya

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce har yanzu a hukumance kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su sanar da ita matakinsu na fita daga cikinta ba.

A ranar Lahadi da hantsi kasashen uku suka fitar da sanarwa cewa sun fice daga kungiyar saboda ta gaza taimaka musu wurin shawo kan rashin tsaron da ke addabasu da ma sauran kalubalen da suke fama da su.

"Har yanzu Hukumar ECOWAS ba ta samu bayani a hukumance daga kasashen uku ba da ke nuna cewa sun fita daga cikinta," a cewar wata sanarwa da ECOWAS ta wallafa a shafinta na X.

Kungiyar ta ce ta yi mamakin "wannan mataki."

ECOWAS ta kara da cewa tana "aiki babu kakkautawa da wadannan kasashe domin ganin an dawo da tsarin mulki."

"Burkina Faso, Nijar, da Mali mambobinmu ne masu matukar muhimmanci kuma hukumar nan za ta yi bakin kokarinta wurin samar da mafita ga rikicin siyasar da suke ciki."

TRT Afrika