A ranar Talata 18 ga watan Yuli ne aka wayi gari da karin farashin man fetur a Nijeriya abin da ya sa 'yan kasar suke ta kokawa kan halin da wannan mataki zai jefa su a ciki.
Gidajen mai sun sauya farashin fetur daga sama da naira 500 zuwa fiye da naira 600 kan kowacce litar mai daya, kuma farashin ya danganta ne daga jiha zuwa jiha.
Shugaban kamfanin man fetur na Nijeriya, NNPCL, Malam Mele Kyari ya ce farashin fetur ya tashi ne saboda "kasuwa ce take yin halinta" bayan gwamnatin kasar ta cire tallafin man fetur a watan Mayu.
Wannan mataki na nufin daga yanzu ‘yan kasuwa ne za su sayo man fetur kuma su sayar da shi kan farashin da suka kayyade.
Tashin farashin ya kara tsadar rayuwa a tsakanin 'yan kasar inda kwana guda kafin karin hukumar kididdiga ta Nijeriya ta fitar da sanarwar cewa an samu karuwar hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
Yanzu dai 'yan Nijeriya sun shiga laluben hanyoyin da za su bi domin samun saukin wannan matsala.
TRT Afirka Hausa ta tattauna da masana tattalin arziki kan hakan, inda suka fayyace wasu matakai da suke gani za su sama wa 'yan kasar sa'ida:
Dakatar da abubuwan da ba su zama wajibi
Masana tattalin arziki irin su Abdullahi Abubakar da ke koyarwa a Sashen Tsimi da Tanadi na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, ya bayyana cewa ya kamata mutane su dakatar da duk wani abu da bai zama wajibi ba domin su samu sauki.
"Akwai abubuwa da dama wadanda rayuwa za ta ci gaba ko ba a yi su ba amma wasu jama’a na tilasta wa kansu cewa dole sai sun yi," in ji shi.
Ya kara da cewa "wasu mutanen ba sa iya wata uku ba su sauya wayar salularsu ba, amma hakan ba dole ba ne. Kazalika akwai wadanda ba sa iya shekara guda da mota daya su ma sai sun yi kokarin canza ta."
Malamin ya ce haka kuma akwai wadanda duk wata sai sun yi sabon dinki ko kuma yin wata hidima wadda ba dole ba ce, yana mai cewa "dakatar da irin wadannan zai bai wa mutane damar kashe kudinsu a fannin da ya wajaba a kansu sanna su samu saukin rayuwa."
Tafiye-tafiye sai sun zama dole
A cewar masanin, akwai bukatar mutane su sauya yadda suke rayuwa musamman masu son zuwa unguwa ko tafiye-tafiye a-kai-a-kai wadanda da ba su zama wajibi ba.
Ya bayyana cewa ko mene ne ya faru idan mutum ya tsara rayuwarsa, zai samu sauki.
“Ya kamata masu yawan tafiye-tafiey don halartar bukukuwan da ba su zama wajibi ba su rage. Za ka ga mata sun tafi biki gari mai nisa tare da ‘ya’ya da yawa. Ana kashe kudin mota mai yawa tare da bayar da gudunmawa ta biki.
“Maimakon tafiya biki, zai fi kyau a tura wa mai bikin kudin ko gudunmawar kawai ba sai an je ba,” in ji shi.
Rage almubazzaranci da takaita hidimomin gida
Akwai bukatar magidanta su hada kai da iyalansu domin nemar wa kawunansu sauki bisa karfin aljihunsu.
Mutane da dama suna almubazzaranci musamman wurin dafa abinci da a wasu lokuta har zubarwa ake yi, ko kuma barnata kayan hadin abinci kamar su man gyada wadanda su ma kayayyaki ne masu tsada.
Sannan ya kamata a ririta makamashi iri daban-daban da ake amfani da su a gidaje kamar wutar lantarki da gas ko kalanzir. Misali, bai kamata a kunna kwan lantarki ba idan ba amfani ake da shi ba, ko kuma a kunna gas a bar shi yana karewa ba tare da an yi aiki da shi ba.
Akwai hidimomin gida na yau da kullum da dama wadanda suka kamata mutane su rage domin samun sauki.