Hukumomi a Amurka sun tuhumi fitacciyar mai amfani da shafukan sada zumunta ta Ghana Mona Faiz Montrage da laifin zambatar wasu mutane $2m ta hanyar soyayyar bogi.
Bayanan da wata Kotun gunduma ta Kudancin New York ta fitar ranar Litinin sun bayyana cewa ana zargin Mona, wadda aka fi sani da Haji4Real, da aikata laifuka shida na zambar kudi daga wurin wasu maza marasa aure ta hanyar kulla soyayya da su ta karya.
Wata sanarwa daga Antoni Janar na birnin, Damian Williams, ta ce “Kamar yadda ake zargi, Mona Faiz Montrage, mamba ce ta wani gungun masu aikata laifuka da ke yaudarar Amurkawa ta hanyar damfara da sunan soyaya.
“Irin wannan damfara tana yin tasiri ga rayuwar mutanen da aka yi wa ta fannin lafiyar kwakwalensu da kuma kudadensu. Jami’an tsaronmu sun yi kokari sun kamo ta daga wata kasa inda suka kawo ta Amurka domin ta fuskanci shari’a.”
Rahotannin sun ce a watan Nuwamban 2022 aka kama Mona daga Birtaniya aka kai ta Amurka inda aka tuhume ta a watan nan na Mayu.