An soma shari’ar waɗanda ake zargin a ranar Juma'a a gaban Mai Shari’a J.K Omotosho na Babbar Kotun Abuja. / Hoto: VON

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da gurfanar da ‘yan ƙasar China takwas da kuma ɗan Nijeriya ɗaya a gaban kotu kan zarginsu da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Gwamnatin ƙasar ta sanar da hakan a wata sanarwa da ma’aikatar kula da albarkatun ƙasa ta Nijeriya ta fitar a ranar Juma’a.

A sanarwar da ta fitar, ta ce an kama mutanen ne kan zarginsu da ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Lokpaukwe da ke Umuchieze a Ƙaramar Hukumar Umunneochi ta Jihar Abia.

Ma’aikatar ta bayyana cewa jami’an tsaron farin kaya na NSCDC waɗanda aka horas na musamman domin yaƙi da masu gudanar da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne suka aiwatar da kamen, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Nijeriya ta ruwaito.

An soma shari’ar waɗanda ake zargin a ranar Juma'a a gaban Mai Shari’a J.K Omotosho na Babbar Kotun Abuja.

Gwamnatin Nijeriyar ta shigar da su ƙara kan zarge-zarge uku waɗanda suka haɗa da haƙar ma’adinai ba tare da izini ba da kuma kawo cikas da ga aikin haƙar ma’adinan da ake yi bisa ƙa’ida da sauransu.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da Shen Yongchan, Mo Baixian, Xiao Bin, Huang Xu Fa, Ma Bingli, Yang Jian, Li Peiyin, Que Wenyong, Hiyk Edward Desmond da kuma kamfaninsu mai suna WANDA Company Limited.

TRT Afrika da abokan hulda