Gwamnonin sun ce idan ba a bi a sannu ba Nijeriya za ta koma kamar ƙasar Venezuela. / Hoto: Facebook/ Bala Mohammed

Gwamnonin jam’iyyar hamayya a Nijeriya sun bukaci a samar da ’yan sandan jihohi a kasar saboda a cewarsu ta haka ne kawai za a iya shawo kan matsalolin tsaron da kasar ke fama da su.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar PDP Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ne ya shaida wa manema labarai haka a Abuja bayan wani taro da kungiyar ta yi ranar Litinin.

Cikin gwamnonin da suka halarci taron har da Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara da Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde da Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri da Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang da Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da Gwamna Kefas Agbu na jihar Taraba da kuma Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki.

Sai kuma Mataimakin Gwamnan jihar Delta Monday John Onyeme. Kazalika gwamnonin sun koka kan tsadar rayuwa da kuma karyewar darajar naira.

Haka kuma sun bukaci kwamitin tattalin arziki na gwamnatin tarayya da ya lalubo hanyoyin magance kalubalen.

Gwamna Bala Mohammed ya koka kan matsalar tsadar rayuwa da kuma karyewar darajar naira, inda ya siffanta abin da matsalar karyewar tattalin arzikin da ya taba faruwa a kasar Venezuela.

“Mun kama hanyar zama Venezuela.”Kungiyar gwamnonin PDP ta bukaci gwamnatin tarayyar kasar da ta dauki matakan gaggawa dangane da halin matsin da ’yan Nijeriya suke ciki kan tattalin arziki da matsalolin tsaro.

TRT Afrika