Shugaba Tinubu ya ce bai wa ƙananan hukumomi damar sarrafa kuɗaɗensu kai-tsaye  za ta kawo ci gaba ga mazauna karkara./Hoto:Ofishin shugaban Nijeriya

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kafa wani kwamiti mai mutum goma da zai tabbatar da bin hukuncin Kotun Koli na bai wa kananan hukumomi cin gashin kansu.

A ranar Talata ne Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume ya ƙaddamar da kwamitin mai ƙunshe da ɓangarori 10 don tabbatar da cewa an bi hukuncin da Kotun Ƙoli ta aiwatar a ranar 11 ga watan Yulin 2024 da ya ce a dinga bai wa ƙananan hukumomin Nijeriya kuɗaɗensu kai-tsaye.

Sanarwar da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar ta ce: “Babban aikin kwamitin shi ne tabbatar da cewa an bai wa ƙananan hukumomi cikakken ‘yancin cin gashin kansu, da ba su damar yin aiki sosai ba tare da katsalandan ɗin gwamnatocin jihohi ba.

“Wannan matakin dai ya yi daidai da kokarin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an aiwatar da tsarin da ya dace ga tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki, wanda ya amince da kananan hukumomi a matsayin mataki na uku na gwamnati,” in ji sanarwar.

Mambobin kwamitin sun haɗa da:

  • Sakataren Gwamnatin Tarayya a matsayin Shugaban Kwamiti
  • Ministan Kudi da na Tattalin Arziki - Mamba
  • Atoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a - Mamba
  • Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki
  • Babban Akanta na Gwamnatin Tarayya
  • Gwamnan Babban Bankin Nijeriya
  • Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗi
  • Shugaban Hukumar Tarawa da Kason Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa
  • Wakilan Gwamnnoni
  • Wakilan Ƙananan Hukumomi

Waiwaye

A ranar 11 ga watan Yuli ne alkalin Kotun Koli Mai Shari'a Emmanuel Agimya umarci gwamnatin tarayya ta riƙa tura wa ƙananan hukumomin ƙasar 774 kuɗaɗensu kai-tsaye domin su riƙa gudanar da harkokinsu.

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ce ta shigar da ƙara inda ta roƙi Kotun Ƙolin ta bari a riƙa tura wa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu ba tare da katsalandan ɗin gwamnoni ba.

Kazalika alƙalin ya ce naɗin da gwamnoni suke yi wa shugabannin ƙananan hukumomi na riƙo ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya, yana mai cewa alhakinsu ne su gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi.

Tuni dai har wasu jihohin sun fara shirya zaɓukan ƙananan hukumomi a fadin ƙsar har ma an gudanar da na wasu jihohin.

TRT Afrika