Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar.
Kotun Kolin ta tabbatar da hakan ne a hukuncin da ya zama na karshe da ta yanke a yau Alhamis a kan zaben shugaban Nijeriya wanda Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour ke kalubalanta.
Tawagar alkalai bakwai ce ta yanke hukuncin bayan yin nazari a kan hukunce-hukuncen da kotunan baya suka yanke.
Zaman kotun na karshe ya samu halartar shugabannin duka manyan jam'iyyun kasar da sauran manyan 'yan siyasa.
Tun farko Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP sun nemi Kotun Kolin ta soke zaben Bola Tinubu wanda kotun sauraren kararrakin zabe ta tabbatar da nasararsa a matsayin shugaban kasa a zaben 2023.
Kazalika sun dage cewa Shugaba Tinubu bai cancanci tsayawa takara ba, kuma bai samu ƙuri'u mafi rinjaye a zaben da aka gudanar a Nijeriya ba.
Atiku Abubakar ya gaya wa Kotun Kolin cewa takardun kammala Jami'ar Chicago State University da Shugaba Tinubu ya mika wa hukumar zaben Nijeriya, INEC, don tsayawa takara na jabu ne.
A watan Fabrairu aka gudanar da zaben shugaban kasar kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, INEC, ta ayyana dan takarar jam'iyyar APC Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara inda samu kuri'a 8,794,726 -- wato kashi 37 na kuri'un da aka kada.
INEC ta ce Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ne yake biye masa da kuri'a 6,984,520 -- kashi 29, yayin da dan takarar Jam'iyyar Labour Peter Obi ya samu kuri'a 6,101,533 -- kashi 2