Fadar shugaban ƙasar ta ce “da farko dai akwai buƙatar mu fayyace cewa gwamnatin Shugaba Tinubu tana girmama ra’ayoyin ƴan Nijeriya.

Fadar shugaban ƙasar Nijeriya ta yi ƙarin bayani kan abin da take nufi da sayen “jirgin ruwan kasaita na shugaban ƙasa” da za a yi a cikin ƙwarya-ƙwaryan ƙarin kasafin kuɗi na shekarar 2023 da ta gabatar wa Majalisar Dokoki.

“Akwai buƙatar yin ƙarin bayani kan sayen “jirgin ruwan shugaban ƙasa” da aka saka a ƙarin kasafin kuɗin 2023 da aka kai wa majalisa, sakamakon ce-ce-ku-cen jama’a da hakan ya jawo,” in ji sanarwar da aka wallafa a shafin X na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Batun sayen jirgin ruwan wanda a cikin kasafin da aka gabatar wa majalisa aka kira shi da “jirgin ruwan kasaita na shugaban ƙasa” ya yi matuƙar tayar da ƙura a Nijeriya.

Fadar shugaban ƙasar ta ce “da farko dai akwai buƙatar mu fayyace cewa gwamnatin Shugaba Tinubu tana girmama ra’ayoyin ƴan Nijeriya a kan dukkan al’amuran da suka shafi jama’a.”

Sanarwar fadar ta yi wasu bayanai huɗu a kan abin da sayen “jirgin ƙasaita na shugaban ƙasa” ke nufi, kamar haka:

1. Idan aka ce Jirgin Ruwan Ƙasaita na Shugaban Ƙasa ana nufin wani Jirgin Yaƙin Sojin Ruwa mai wasu kayayyakin tsaro na musamman saboda yin muhimman ayyuka, ba wai don amfanin Shugaban Ƙasar ba.

Ana kiransa Jirgin Ruwan Kasaita na Shugaban Kasa ne saboda muhimman abubuwan tsaro da yake ɗauke da su.

2. Rundunar Sojin Ruwa ce ta yi odar jirgin ruwan tun a lokacin gwamnatin da ta gabata. Shugaba Tinubu ya sha cewa gwamnatinsa za ta ɗora kan ayyukan da gwamnatin baya take yi na abubuwan da ya gada daga fannin kadarori har na ayyuka.

3. Buƙatar biyan kuɗin sayen jirgin ruwan kuwa na daga cikin abin da ofishin Babban Hafsan Rundunar Sojin Ruwa ya gabatar ne ga Ma’aikatar Tsaro. Jumullar abin da aka buƙata shi ne naira biliyan 200, amma Shugaban Ƙasa ya amince ne kawai da naira biliyan 62.

4. Shugaba Tinubu yana mayar da hankali a kan tabbatar da tsaron ƙasarmu da iyakokinta na ruwa. Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin jagorancinsa tana zuba jari sosai don bunƙasa tattalin arziki a fannin man fetur da isakar gas da tattalin arzikin teku.

Ce-ce-ku-cen ‘yan Nijeriya

Tun da farko batun sayen wannan jirgin ruwan ƙasaita na shugaban ƙasa da na sabbin motocin alfarma ga Uwargidan Shugaban Ƙasar, Remi Tinubu da niyyar kashe naira biliyan 28 don gudanar da al'amuran fadar shugaban kasa daga cikin ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗin daka gabatar sun yamutsa hazo a Nijeriyar.

Mutane sun yi ta sukar lamarin suna danganta shi danganta shi da halin da ƙasar ke ciki na matsin tattalin arziƙi.

Wasu kakafen watsa labaran ƙasar ma sun rawaito cewar Majalisar Wakilan Tarayya tuni ta yi watsi da ƙin amincewa da wasu daga cikin buƙatun da Fadar Shugaban Ƙasar take son yi da kuɗaɗen ƙarin kasafin da ta gabatar.

TRT Afrika