Masu sharhi kan lamuran yau da kullum a Nijeriya da ma wasu ‘yan kasar suna ta tofa albarkacin bakinsu kan salon da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ke dauka na aiwatar da wasu ayyuka da garanbawul cikin hanzari.
Cikin kasa da wata daya da rantsar da shi, Shugaba Tinubu ya yi wasu sauye-sauye da daukar wasu matakai da suka sa ja hankalin ‘yan kasar.
Baba go fast! Wannan shi ne ma sabon sunan da wasu ‘yan kasar suka sanya wa Shugaba Tinubu sakamakon yadda yake daukar matakai da gudanar da gwamnatinsa tun ma kafin ya nada ministoci.
Sabon shugaban kasar na Nijeriya, wanda ya sha rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayun 2023, ya soma mulki da karfinsa, inda kawo yanzu ya dauki matakai a bangarori da dama cikin, abin da wasu za su iya cewa kiftawa da Bisimillah.
Abu na farko da Shugaba Tinubu ya fara yi tun a wajen jawabin rantsuwar kama mulki shi ne ya bayyana karara cewa an cire tallafin man fetur.
Duk da cewa lamarin ya harzuka mutane har ma Kungiyar Kwadago ta yi shirin tafiya yajin aiki, shugaban ya yi gaggawar shawo kansu inda suka jingine yajin aikin.
Sai kuma ya zauna da ma’aikatan lafiya da suke yajin aikin su ma, inda ya rarrashe su suka janye.
Dakta Kabiru Sa'idu Sufi, mai sharhi kan lamuran yau da kullum kuma Malami a Sashen Koyar da Harkokin Siyasa na Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, ya ce irin wadannan matakai ake so shugaba ya dauka a zarar ya karbi mulki domin 'yan kasar su san cewa da gaske yake.
“Abu ne da ake bukatarsa, saboda ya dau hankalin jama’a kuma ya dawowa da mutane kwarin gwiwar da suke da shi a kansa da cewa shugaba ne da ya zo da niyyar kawo sauyi, kuma zai iya kawo sauyin,” in ji mai sharhin.
Masanin sha’anin mulki Dakta Sufi ya ce “wannan mataki na daga cikin abubuwan da ake bukata dama.
"Ba a bukatar jan kafa musamman wajen harhada wadanda za su iya taimakawa wajen kawo sauyi.
“Hakan ya nuna cewa yana da sani da jajircewar hada tawagar aiki da za su iya samar da sauyi,” ya ce.
A hannu guda kuma, zaben shugabancin majalisar dokokin kasar ya nemi zama rigima tsakanin masu takara, sai dai Shugaba Tinubu ya rarrashi wasu fitattun 'yan majalisar wakilan Nijeriya guda biyu da ke gaba-gaba wajen neman shugabancin majalisar.
A ganawar da ya yi da su kafin zaben, Shugaba Tinubu ya sa Honorabul Muktar Betara Aliyu da Honorabul Yusuf Gagdi sun janye takararsu kuma sun goyi bayan Tajudeen Abbas wanda ya yi nasara.
“Hakan na nuna cewa dadewar da ya yi a cikin siyasar kasar nan da hulda da shugabannin jam’iyyu da na al’umma a lungu da sako na kasar nan, suna yi masa amfani wajen ba shi damar daukar hukunce-hukunce cikin lokaci kankani kuma cikin sauri.
“Wannan shi ke nuna alamun lallai cakwai kwarewa da kuma sanin makamar mulki da kuma cewa an shirya masa,” kamar yadda Dakta Sufi ya kara da cewa.
Kazalika Shugaba Tinubu ya dakatar da kuma maye gurbin wasu manyan jami’an gwamnati, ciki har da shugaban Babban Bankin Nijeriya CBN, Godwin Emefiele, wanda aka nada kan kujerarsa a zamanin Shugaba Goodluck Jonathan.
Sannan ya dakatar shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa EFCC, AbdulRasheed Bawa.
Bayan nan sai kuma ga CBN ya ayyana daidaita farashin kasuwar hada-hadar kudin kasashen waje.
Haka kuma Shugaba Tinubu ya kuma rika ganawa da manyan mutane daga bangarori daban-daban da suka hada da ‘yan siyasa (na jam’iyyarsa da kuma na jam’iyyun hamayya), da malaman addini, da sarakunan gargajiya da ‘yan kasuwa da saura masu ruwa da tsaki don saita kasar.
Ana cikin haka, sai ga abin da wasu ke kira Tsunami! A makon nan shugaban kasar ya yi wa hafsoshi da sauran shugabannin tsaro na kasar ritaya nan take.
Sai ya maye gurbinsu da sababbi, ciki har da babban mai ba shi shawara kan sha’anin tsaro da kuma babban sifeto ‘yan sanda.
Hakan ne ya sa wasu ke ta tsokaci cewa idan har aka Shugaba Tinubu ya dore a kan wannan turba, watakila rayuwar ‘yan Nijeriya ta inganta.
“Wannan ne abu na farko dama da ake bukata a wajen shugabanci, sanin cewa akwai mutanen da idan an dauko su, da su ne za a kai ga nasara.
“Kuma hakan ya nuna cewa lallai mutanen da ake daukowa din idan aka ci gaba da zakulo irin su to akwai yiwuwar samun nasarar sauyi cikin lokaci kankani,” a cewar Dakta Sufi.
Abu na gaba
Masu sharhi na ganin abin da ya kamata a duba yanzu shi ne a yi fatan Shugaba Tinubu ya ci gaba da wannan zafi-zafin da ya dauko din kar a bari abubuwa su ja baya.
“A halin yanzu abin ya ja hankali kuma ya sa mutane suna ta yabawa da kuma sa rai
Don haka ka da a sare musu gwiwa da wannan yabo da sa rai, idan da hali ma a kara a kai tun da abin da kasar take bukata Kenan,” in ji Malamin Kwalejin.
‘Yan Nijeriya da suke ta tsokaci a shafukan sada zumunta na ganin a baya jan kafa ya jawowa kasar koma-baya inda komai ma aka rasa wane hali yake tafiya.
Masana sun ce a yanzu ya kamata shugaban kasar ya mayar da hankali don ganin duk abubuwan da aka yi alkwari a kansu a yakin neman zabe to lallai a gaggauta cika su don yanzu abin da jama’a ke jira su gani kenan.
Na biyu dawo wa da kasar martabarta, mutane na ganin darajar Nijeriya ta ragu idan aka yi la'akari da tabarbarewar lamura.
“Ya kamata gwamnati ta jajirce wajen daina sayen tataccen man fetur daga waje bayan ta sayar da danyensa.
“Sannan a samar da ci-gaba ta fuskar tsaro saboda zai gyara abubuwa da yawa kamar tattalin arziki da tsaro da lantarki da ababen more rayuwa da ilimi da zai inganta zamantakewar 'yan kasa,"in ji Dakta Sufi.