Gwamnatin mulkin sojin Mali ta ce za ta gudanar da zaɓe ne kawai sannan ta miƙa mulki a hannun farar-hula idan yanayin tsaron ƙasar ya inganta.
Firaiministan ƙasar wanda sojoji suka naɗa ne ya bayyana haka ranar Alhamis da tsakar dare.
"Dole tsaro ya yi matuƙar inganta kafin a gudanar da zabe," in ji firaminista Choguel Kokalla Maiga, a wani jawabi da aka watsa ta gidajen talbijin da soshiyal midiya, ba tare da ya bayyana takamaimai ranar da za a yi zaɓen ba.
Maiga ya ce mutanen da ke kiraye-kiraye a gudanar da zaɓe nan ba da jimawa da suna yi ne domin biyan buƙatun "maƙiyan Mali".
Jawabin nasa na zuwa ne a yayin da hukumomi a ƙasar ta Mali suka haramta wa 'yan jarida ɗaukowa da bayar da rahoto kan harkokin jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyi. Wannan ya zo ne kwana ɗaya bayan da ta dakatar da harkokin siyasa a ƙasar har sai ila-ma-sha Allahu.
Gwamnatin ta ba da odar ne daga ofishin babar hukumar sadarwa, wadda aka yaɗa a soshiyal midiya a yammacin Alhamis.
Sanarwar ta ce haramcin ya shafi duka nau'in gidajen jaridu, gami da na talabijin, da na rediyo, da na intanet, da na takarda.
Mali ta yi fama da julin mulkin soji guda biyu tun shekarar 2020, wanda ya haifar da rashin zaman lafiya da ya watsu a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka a 'yan shekarun nan.
Baya ga matsalolin siyasa, ƙasar tana fama da mafi munin rikicin ta'addanci daga mayaƙa masu alaƙa da Al-Qaida.
Martanin 'yan jarida
A yanzu ba a san faɗin haramci kan 'yan jarida ba, ko yadda za a zartar da shi a zahiri. Kuma ba a san ko za a ci gaba da barin 'yan jarida su ba da rahoton batutuwa kamar na tattalin arziƙi ba, wanda suke da alaƙa da siyasa, kuma ba a san ko waye zai sa ido kan ayyukan nasu ba.
Babbar ƙungiyar da ke wakiltar 'yan jaridu a ƙasar ta yi watsi da haramcin.
Ƙungiyar mai suna Maison de le Press, ko Gidan 'Yan Jarida, ta ce ta yi watsi da odar kuma tana kira da 'yan jaridu da su ci gaba da bayar da rahoto kan siyasa a Mali.
Sa'annan ta yi kira gare su da su yi "tsayin-daka, su ci gaba da haɗa kai, don kare haƙƙoƙin 'yan ƙasar na samun labarai.”
Fargaba kan 'yancin ɗan'adam
Hukumar kula da haƙƙin ɗan'adam ta Mali ta bayyana baƙin cikinta da damuwarta kan hukuncin a wata sanarwa da ta wallafa ranar Alhamis. Hukumar ta yi gargaɗin cewa hukunci zai iya zama mai cutarwa.
Hukumar ta kuma ƙara da cewa, “Maimakon kwantar da guguwar tunzurin jama'a, haramcin zai taƙaita haƙƙoƙin ɗan'adam, kuma zai iya haddasa tashin hankali, wanda ƙasar ke ƙoƙarin kaucewa".
Takunkumin kan 'yan jarida yana zuwa ne bayan wata oda da gwamnatin sojan ta bayar ranar Laraba, na dakatar da duka ayyuka jam'iyyun siyasa har sai sanda ta waiwaye su, inda ta ce ta yi ne don kiyaye zaman lafiyar al'umma.
An watsa labarin a gidan talabijin na ƙasa yayin da al'ummar ƙasar ke bukukuwan Sallah ƙarama, wanda ya zo bayan azumin watan Ramadana.
Kanal Assimi Goita, wanda ya hau mulki bayan juyin mulki karo na biyu a ƙasar a 2021, ya yi alƙawarin dawo da ƙasar turbar dimukuraɗiyya a farkon 2024. Amma a Satumbar bara, gwamnatin sojin ta soke zaɓukan da aka shirya yi a Fabrairun 2024, inda ta ce akwai matsalolin shirin zaɓen.