Gwamnatin Nijeriya za ta soma raba wa ƴan ƙasar hatsi a wannan mako kamar yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni, a cewar Ministan Harkokin Noma.
Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin da maraice.
Ministan ya ce gwamnatin ƙasar tana sane da mawuyacin halin da ƴan ƙasar suke ciki kuma tana tausaya musu, yana mai cewa "na fahimci girman yanayin da ake ciki, musamman ganin yadda ake wawashe kayan abinci daga rumbuna."
A cewar Sanata Kyari, wannan hali ne ma ya sa "za mu soma raba tan 42,000 na hatsi, kamar yadda shugaban ƙasa ya amince a yi, a jihohi 36 da ke faɗin ƙasar nan a wannan mako."
"Muna aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar NEMA da rundunar DSS domin tabbatar da cewa hatsin ya isa wurin mutanen da suka cancanta. Kazalika, za a shigar da shinkafa tan 58,500 kasuwa wadda masu casar shinkafa za su samar da zummar samun sauƙin farashi," in ji Minista Kyari.
Gwamnatin Nijeriya ta sanar da wannan mataki ne kwana guda bayan Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar (NEMA) ta umarci jami'anta da ke faɗin Nijeriya su sanya ƙarin matakan tsaro a rumbunanta bayan wasu mutane sun daka wawason kayan abinci a wasu rumbunan gwamnati.
A baya-bayan nan, wasu ƴan Nijeriya sun riga wawason kayan abinci daga rumbunan gwamnati da manyan motocin ɗaukar kaya na wasu ƴan kasuwar ƙasar a yayin da ake ta ƙorafi game da tsadar rayuwa.