Gwamnatin Nijeriya ta yi tayin bai wa ma'aikatan ƙasar N62,000 duk wata a matsayin mafi ƙarancin albashi maimakon N60,000 da ta yi musu tayi tun da farko.
Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya George Akume ne ya bayyana haka ranar Juma'a da daddare a taron da ya jagoranci sauran manyan jami'an gwamnati da ɓangarori masu zaman kansu.
Ya ce za su miƙa wa Shugaba Bola Tinubu wannan shawara domin ya aike wa majalisun dokokin ƙasar don su mayar da ita doka.
Sai dai ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar ta buƙaci a riƙa bai wa ma'aikata N250,000, maimakon N494,000 da a baya ta dage cewa dole gwamnati ta biya.
Hakan na faru ne a yayin da ƙungiyar gwamnoni ta Nijeriya ta ce gwamnonin ba za su iya biyan N60,000 da gwamnatin tarayyar ta yi tayin biyan ma'aikatan tun da farko ba.
Kawo yanzu dai ɓangarorin biyu ba su cim ma matsaya game da albashi mafi ƙaranci ba, ko da yake sun ce za su ci gaba da tattaunawa don samun mafita.
A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne ƙungiyoyin ƙwadago na Nijeriya suka tsunduma yajin aiki a faɗin ƙasar bayan sun kasa samun matsaya da gwamnatin tarayya kan mafi ƙarancin albashi da kuma buƙatarsu ta neman a janye ƙarin da aka yi na kuɗin lantarki.
Yajin aikin ya kawo tsaiko a harkokin kiwon lafiya da kasuwanci da sufuri, inda har ma ƙungiyar ƙwadago ta katse babban layin lantarki na Nijeriya.