Sai dai gwamnatin ta ja hankalin ƴan kasuwar da su mutunta wannan farashin da aka tsayar. Hoto: Getty

Gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar ta karya farashin kuɗin buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50, wanda a da kudinsa yake jaka 16.500 ta CFA, a yanzu kuma za a ringa sayar da shi jaka 13.500.

Ma'aikatar Kasuwanci ta Ƙasar ce ta sanar da hakan a yayin wani taro da Ministan, Malam Asmane Saidou ya gudanar tare da ƙungiyoyin ƴan kasuwar ƙasar.

Sai dai wannan sabon farashi ya bambanta daga wannan jihar zuwa wata, inda a Yamai za a sayar da buhun a kan jaka 13.500 na CFA.

Farashin sauran jihohin sun haɗa da:

  • Dosso 13.675 CFA
  • Tawa 13.825 CFA
  • Maradi 13.925 CFA
  • Zinder 14.000 CFA
  • Diffa 14.375 CFA
  • Agadez 14.125 CFA
  • Atillaberi 13.650 CFA.

Ministan Kasuwanci na Nijar

Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan matakin ne bayan ta zauna da ƴan kasuwar masu manyan motocin dakon kaya aka tattauna da su kafin ɗaukar wannan matakin.

Sai dai gwamnatin ta ja hankalin ƴan kasuwar da su mutunta wannan farashin da aka tsayar.

Nijar tana shigar da shinkafa daga ƙasashen waje ne inda ƴan kasuwa ke amfani da tashar ruwan Tekun Jamhuriyar Benin wajen shigar da kayayyakinsu zuwa cikin ƙasar.

To sai dai juyin mulkin da sojojin kasar sukayi a watan yulin bara ya sa Jamhuriyar Benin rufe iyakokinta da Nijar bisa umurnin Ƙungiyar Ecowas, wadda ta ƙaƙaba wa Nijar takukumai, lamarin da a baya ya haddasa ƙarancin shinkafar da sauran ƙayan masarufi, da kuma tashin farashinta a kasuwanni.

Amma rahotanni daga Nijar din na cewa a yanzu abubuwa sun fara daidaita ba kamar watanni shida na baya ba.

TRT Afrika