Sarki Aminu Ado Bayero ne yake zaune a cikin gidan tun bayan fara dambawar masarutar jihar. Hoto: Masarautar Kano Facebook

Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta ce za ta rusa Gidan Sarki na Nasarawa wanda Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ke ciki.

Ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kwamishinan Shari'a Barista Haruna Isah Dederi ya gabatar jim kadan bayan hukuncin da Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke game da dambarwar Masarautar Kano.

"Don haka ne ma gwamnati ta umarci Kwamishinan 'Yan Sanda da ya fitar da Sarkin ƙananan hukumomin cikin birni guda takwas da aka yi wa murabus daga cikin ginin inda yake keta doka, saboda tuni gwamnati ta kammala shirye-shiryen yi wa gidan kwaskwarima ba tare da ɓata lokaci ba," in ji Barista Haruna Isah Dederi.

A yau Alhamis ne Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke hukuncin rusa dokar da ta sauke Sarki Aminu Bayero.

Amma a jawabin da Dederi ya yi, ya ce gwamnatin jihar Kano ta karɓi hukuncin Babbar Kotun Tarayya game da dokar Masarautun Kano ta 2024, da aka yi wa garambawul kuma tana ganin hakan a matsayin yin biyayya ga tsarin doka.

"Wannan hukuncin ya bayyana ƙarara halascin dokar da 'yan majalisar dokoki suka yi wacce Gwamnan Kano ya sanya wa hannu ranar 23 ga watan Mayu. Hakan na nufin Sarki Muhammadu Sanusi shi ne halastaccen Sarkin Kano," in ji kwamishinan, wanda ya yi jawabin a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya ƙara da cewa "Haka kuma alkalin ya amince da bukatarmu ta tsayawa a inda ake har sai Kotun Daukaka Kara ta saurari karar da aka daukaka a gabanta.

"Abin farin cikin shi ne sanya hannu kan dokar da kuma mayar da Mai Martaba Muhammadu Sanusi an yi su ne ranar 243 ga watan Mayu 2024 kafin hukuncin wucin gadi da aka ba mu ranar 27 ga Mayun 2024."

TRT Afrika