Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta rage kudin Aikin Hajjin bana zuwa cfa 3,258,733 ga ko wane maniyyaci daga cfa 3,603,840 da ta sanar a baya.
Ministan Cinikayya na kasar, Alkache Alhada, ya ce an rage cfa 345,107 daga cikin kudin aikin Hajjin ne bayan hukumomin Saudiyya sun rage kudaden da maniyyata za su biya a kan kudaden wasu abubuwa.
Ministan ya bayyana cewar kudaden da kasar Saudiyya ta fara fitarwa sun yi yawa lamarin ya sa kudin da gwamnatin kasar Nijar ta fitar ya karu.
Da kasar Saudiyya ta rage kudaden kuma, sai gwamnatin Nijar ta rage kudaden da ta sanar, in ji ministan.
Ministan ya ce a baya cfa 933,816 ne kudaden ayyuka da kasar Saudiyya ta fitar, amma a yanzu kasar ta mayar da kudaden Sefa 588,753.
Wani ragin da aka samu kuma shi ne na inshorar maniyyata daga riyal 29 zuwa riyal 28.75.
Alkache Alhada ya ce maniyyatan da suka riga suka biya, za a mayar musu da rarar kudin.