Shugaban Bankin Duniya, David Malpass yana ziyarar aiki ta kwana hudu a Nijar da Togo.
Wata sanarwar da bankin ya fitar ta ce, Mista Malpass zai tauttauna da Shugaba Bazoum Mohammed da masu ruwa da tsaki kan shirin cigban kasar da kuma taimakon da shi Bankin Duniyan ya tanadar wa kasar da kuma yankin Sahel.
Shugaba Malpass zai gabatar da jawabi kan matsayar bankin na duniya da kuma hukumar ba da lamuni ta IMF kan tarukan da za a yi cikin watan Afrilu.
Jami’ar Abdou Moumouni da ke Niamey ce za ta karbi bakuncin jawabin.
A lokacin da yake yi wa Shugaba Bazoum bayani game da shirin ofishin bankin na kasar kan tarbar shugaban Bankin Duniyar, shugaban ofishin bankin na Nijar, Abdul Salam Bello, ya ce baya ga harkar tsaro da cigaba, ziyarar ta shugaban Bankin Duniyar za ta mayar da hankali kan dogaro da kai a fannin abinci.
Har wa wau, shugaban ofishin bakin a Nijar ya ce ziyarar za ta mayar da hankali kan harkar ilimi, yana mai karawa da cewar Shugaban Nijar, Bazoum Mohammed yana da shiri na musamman kan karatun yara mata.