A ranar 3 ga Agustan 1960 ne Nijar ta samu taken kasa daga Faransa. Hoto: Reuters

Daga Awa Cheikh Faye

A kokarin Nijar na watsi da abin da ta gada daga mulkin-mallakar Faransa na taken kasa da yake bayyana tsantsar dogaro kan wani, kaskantarwa, nuna ba a isa ba da wariyar launin fata, ya sa ta kaddamar da sabon taken kasa mai dauke hoto mai armashi da nuna kima da burin cigaban kasar ta Yammacin Afirka.

An soma amfani da sabon taken kasa a Nijar kafin juyin mulkin makon jiya wanda ya kifar da gwamnatin shugaban kasar Mohamed Bazoum da wasu dakarun Fadar Shugaban Kasa suka yi.

Sabon taken kasar da aka kaddamar a ranar 22 ga watan Yunin wannan shekarar - L'Honneur de la Patrie ko Mutuncin Kasarmu ta Gado - ya maye gurbin taken da dan kasar Faransa Maurice Albert Thiriet ya kaddamar mai sunan La Nigérienne, wanda yake dauke da jimlolin da yawa da 'yan kasar Nijar suke yi wa kallon suna tunatar da su halin da suke ciki na mulkin-mallaka wanda ke fifita farar-fata a kansu.

Majalisar Dokokin Nijar ta amince da sabon taken kasar. Hoto: Reuters

Bangarorin taken kasar irin su 'Soyons fiers et reconnaissants/de notre liberté nouvelle' da 'évitons les vaines querelles', na janyo bacin ran jama'ar Nijar.

Farfesa Boube Namaiwa, malami kuma mai bincike a Sashen Nazarin Falsafa na Jami'ar Cheick Anta Diop da ke Dakar, Senegal ya bayyana cewa, wannan sashe na taken kasar ba shi da amfani, yana kuma zagin kasar ne.

Sabuwar makoma

Duk da cewa tunanin amfani da sabon taken kasa ga Nijar ya samu karbuwa a kowanne bangare, taken L'Honneur de la Patrie ya wuce batun yin suna.

NIjar na son dawo da al'adu tarihi da kimarta ta hanyar kaddamar da sabon taken kasar. Hoto: Reuetrs

Mawakin Nijar Jhonel, wanda ya shawara wajen sukar kasashe rainon Faransa, ya tabo wannan batu a shafinsa na Facebook.

Ya rubuta cewa "Yanzun nan na saurari sabon taken kasa. Ba tare da bata wa kowa rai ba, ku ba ni damar bayyana nadamata. Babu wasu kalmomi da ke iya sanya ni fita waje da sassafe. Babu wasu hotuna da suke bayyana fata nagari ga kasata. Babu fasahar waka. Dakikanci da rashin basira kawai."

"Ka ce na farko ba ya wakiltar kasarka saboda 'yan mulkin-mallaka ne suka rubuta shi? Kawai idan ba za ka iya daukaka na 'yan mulkin mallaka ba, to kar ka kaskanta nasu."

Matsawa gaba

Mambar majalisar dokokin Nijar Djoubie Harouna Maty ma ba ta ji dadin sabon taken kasar ba.

Ta shaida wa TRT Afirka cewa "Ba na son wannan sabon take. Ban san yadda zan karanta wannan take ba. Ba wani abu ne na daban ba. A shafukan sada zumunta na ga 'yan Nijar da dama na tattaunawa kan wannan.

Sabon taken kasar na da manufar dasa kishin kasa a zukatan 'yan Nijar. Hoto: Reuters

Harouna Maty ta kuma yi karin haske kan rashin saka kowanne bangare na Nijar a cikin taken kasar, inda ta ce tana fatan za a gyara taken.

"Ya kamata taken kasa ya zama kamar muryar wata mace da za ta yi tasiri kan jaririnta. Idan ka tsincin kanka a wani hali, da ka ji taken kasarka, sai ya zama kamar kana jin muryar wannan uwa ne. Yau, idan akwai wasu 'yan uwa da ba sa jituwa da juna, nakan fada wa kaina, 'wannan uwa, shin ta yi magana sosai?."

Sai dai Farfesa Namaiwa yana ganin sabon taken kasar ya dace da burace-buracen Nijar na yau.

Juyin mulkin makon da ya gabata ya janyo nuna adawa ga Faransa a Nijar da yankin Sahel. Hoto: AFP

Ya ce "ta hanyar wannan sabon taken kasa, dole mu yi kuka sosai mu bayyana damuwarmu, mu sake nazari kan kalmominsa da sakon da yake dauke da shi don kubutar da kawunanmu daga shakar da aka yi mana.

A wannan gaba, mun so mu samar da matani namu na kanmu, matani mai kalmomin da ke magana da mu, kalmomin da ke yabo da kambama mu, kalmomin da ke ciyar da mu gaba."

Nijar ta yi kwaskwarima ga Sashe na 1 na Kundin Tsarin Mulki don shigar da sabon taken kasa na Jamhuriya a wannan shekarar, abin da Farfesa Namaiwa ya kira da "Hanyar ci-gaba ba tare da mantuwa ba".

"Mun yanke hukuncin mu bayar da fifiko ga wannan matani saboda yana ba mu damar barin halin ko-in-kula da tunanin baya mara dadi, sannan mu tambayi kawunanmu ma'anar da ke kunshe a tsohon taken kasar na Nijar," in ji shi.

TRT Afrika