Shugaban Bankin Duniya David Malpass, ya ce bankin yana tallafa wa Nijar wajen horar da malaman makaranta/Photo World Bank

Shugaban Bankin Duniya, David Malpass ya ce bankin zai rubanya tallafin ilimi da yake bai wa Jamhuriyyar Nijar musamman abin ya shafi ilimin yara mata.

“Dole yankin Sahel ya cigaba kafin a iya cewa cigaba ya tabbata,” in ji David Malpass a wani taron manema labarai bayan ya gana da Shugaban Nijar, Bazoum Mohammed a ranar Alhamis.

Ya ce Nijar na da bukata ta gaggawa wajen inganta wutar lantarki da horar da malaman makaranta.

Kazalika wata sanarwar da Bankin Duniyar ya fitar ta ce shugaban bankin da Ministan Ilimin Fasaha da Koyon Sana’a na Nijar, Kassoum Mammane Moctar, sun ce tallafin bankin a fagen ilimin kasar ya hada da sauya ajujuwan laka zuwa na bulo da kuma gina makarantun kwana na mata.

Shugaban Bankin Duniya ya yaba wa kokarin gwamnatin Nijar na inganta ilimi a kasar tare da mayar da hankali kan ilimin mata.

David Palmass ya ce Nijar na da bukata ta gaggawa wajen samun isasshen wutan lantarki

Malpass da yake ziyarar aiki a Nijar ya ce Bankin Duniya ya bai wa kasar tallafi ta hanyar saka kudi dala biliyan 1.2 a hanyar samun makamashi ta ruwa da ta rana.

Shugaban Bankin Duniyar zai je kasar Togo bayan ziyararsa a Nijar.

TRT Afrika da abokan hulda