Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ya ce zai saka fitacciyar 'yar TikTok Murja Ibrahim Kunya a cikin wadanda gwamnatinsa za ta yi wa auren zawarawa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a taron da ya gudanar da 'yan soshiyal midiya a birnin na Kano.
Ya gudanar da taron ne kwana guda bayan ya yi karin nade-nade na masu ba shi shawara na musamman ciki har 'yan soshiyal midiya.
"Akwai Murja Ibrahim Kunya, wacce kowa ya san irin gudunmawar da ta bai wa wannan tafiyar...yadda ta fito tana yayata ayyuka na alheri da wannan gwamnati ke yi, sai mu ce Allah ya sa barka.
"Wannan Murja ita ce ta fara fitowa a cikin 'yan group dinsu ta ce don Allah, don annabi tana so a yi mata aure," in ji Gwamna Abba Gida-Gida.
Labari mai alaka: Sheikh Daurawa ya bayyana matakan auren zawarawa a Jihar Kano
Ya tambayi mahalarta taron cewa: "Matar da ta fito ta ce tana so a inganta Sunnah ta manzon Allah (SAW) abin kyama ce?".
Gwamnan na jihar Kano ya kara da cewa gwamnatinsa za ta jawo mutane irin su Murja a jiki ba za ta wutakanta su ba kamar yadda wasu mutane suke yi.
"Abin da ya sa nake wannan bayani shi ne... idan wasu sun yi Allah wadai da 'yan uwanmu, masoyanmu, to mu muna kira a gare mu baki daya mu ja su a jiki mu rike su mu yi musu addu'a.
Na san dai ba ta nan amma ina gaya mata cewa mun shirya tsaf don yi mata auren zawarawa, ta kawo mana ango mu kuma Idan Allah ya yarda za mu yi abin da ya kamata," in ji Gwamna Abba Kabir Yusuf.