Kamfanin jiragen  sama na Air Mauritius ya soke dukkan zirga-zirgar jiragensa a matsayin riga-kafin guguwar da ta mamayen kasar. / Hotuna: Getty Images  

Mauritius ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tare da rufe makarantu yayin da wata mahaukaciyar guguwa ta tunkaro tsibirin Tekun Indiya ranar alhamis, a cewar ma'aikatar hasashen yanayi.

Guguwar Eleanor ta mamaye kusan kilomita 200 (mil 125) na yankin arewa maso gabashin ƙasar da misalin ƙarfe 4:00 na safe (0000 GMT) kuma tana gudun da ya kai kilomita 20 a cikin sa'a, in ji hukumar kula da yanayi.

“Ana sa ran Iska za ta kada daga yankin kudu maso gabas a gudun da ya kai kusan kilomita 40 cikin sa’o’i 40 kuma zai kai har zuwa kilomita 110, da rana tsaka,” in ji sanarwar.

Babban jami’in kula da filayen saukar jiragen sama na ƙasa da ƙasa ya ce za a rufe tashar, inda kamfanin jigilar kayayyaki na kasar, Air Mauritius ya soke tashin jiragen da aka shirya tafiyarsu a safiyar ranar Alhamis.

Hanyar guguwa

Kazalika an dakatar da zirga-zirgar ababen hawa tare da rufe makarantu.

Ƙasar wacce aka fi saninta da tsibirai masu tsawo da rairayin bakin teku mai ƙayatarwa da shuɗin ruwan tekun da duwatsu, tana kan hanyar da guguwa ke bi lokaci zuwa lokaci.

A watan Janairu, guguwar Belal ta kashe mutum ɗaya, kazalika ta bar dubban mutane cikin rashin wutar lantarki tare da nutsar da gine-gine da kuma haifar da cunkoson ababen hawa.

A kan samu aƙalla afkuwar guguwa ko mahaukaciyar guguwa sau 12 a kowace shekara a yankin kudu maso yammacin Tekun Indiya a tsakanin watan Nuwamba zuwa Afrilu.

A watan Fabrairun shekarar da ta gabata ne, Mauritius ta fuskanci mamakon ruwan sama da kuma iska mai ƙarfin gaske da guguwar Freddy, waɗanda suka yi sanadiyar salwantar da rayuka da haifar da ɓarna a ƙasashen yankin kudu maso gabashin Afirka, da suka hada da Malawi da Mozambique da kuma Madagascar.

TRT Afrika