Kwamitin ya bayyana cewa an rage kuɗin Aikin Hajjin ne domin cika alƙawarin da Shugaba John Dramani Mahama ya ɗauka domin sauƙaƙa wa maniyyata. / Hoto: AA

Kwamitin Aikin Hajji da Shugaba John Dramni Mahama ya sake nazari kan kuɗin Aikin Hajjin bana ya sanar da rage kuɗin Aikin Hajjin daga GH¢75,000 zuwa GH¢62,000.

Kwamitin ya bayyana cewa an rage kuɗin Aikin Hajjin ne domin cika alƙawarin da Shugaba John Dramani Mahama ya ɗauka domin sauƙaƙa wa maniyyata.

Haka kuma kwamitin ya bayyana cewa an samu nasarar samun wannan rangwamen ne bayan wata tawaga ta musamman da gwamnatin Ghana ta aika zuwa Saudiyya domin tattaunawa da masu kula da maniyyata domin magance duk wasu matsaloli da maniyyatan ke fuskanta.

A yayin da yake magana kan wannan batu, shugaban kwamitin da sake nazari kan kuɗin Aikin Hajjin Alhaji Collins Dauda wanda shi ne ɗan majalisa da ke wakiltar Asutifi South a yankin Ahafo ya jaddada irin kyakkyawan kudiri da shugaban Ghana ke da shi kan sauƙaƙa wa maniyyata ta ɓangaren kashe kuɗi.

Dama tun a lokacin yaƙin neman zaɓe shugaban na Ghana ya yi alƙawarin sauƙaƙa wa maniyyata.

Sannan kwanaki bayan rantsar da shi ya sanar da shirye-shiryen bayar da ƙarin kwana ɗaya a yayin shagulgulan bikin Ƙaramar Sallah da kuma rage kuɗin Aikin Hajji ga Musulman ƙasar.

TRT Afrika