Ghana da Bahamas sun sa hannu kan yarjejeniyar shiga ƙasashen juna ba tare da biza ba

Ghana da Bahamas sun sa hannu kan yarjejeniyar shiga ƙasashen juna ba tare da biza ba

Matakin zai bai wa ƴan ƙasashen biyu damar tafiye-tafiye tsakaninsu ba tare da biza ba.
An sa ran wannan yarjejeniyar za ta bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen biyu:Hoto/Twitter Nana Akufo Addo

Gwamnatin Ghana da takwararta ta Bahamas sun sa hannu kan yarjejeniyar shiga ƙasashen juna ba tare da biza ba.

Yarjejeniyar, wacce aka sanya wa hannu ranar 31 ga watan Janairu amma aka sanar da ita ranar Alhamis, na nufin inganta kasuwanci da alaƙar yawon buɗe ido, ta hanyar kawar da duk wani shinge ga ƴan Ghana da ke son zuwa Bahamas da ƴan Bahamas da ke son zuwa Ghana.

Yarjejeniyar za ta shafi duk masu ɗauke da fasfo na Ghana da Bahamas da suka haɗa da manyan jami’an gwamanti, da jami’an diflomasiyya da sauran ƴan ƙasashen.

Sanarwar ta bayyana cewa an jan hankalin hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen sama da kamfanonin jirage na ƙasashen kan sabon matakin don kaucewa jefa matafiya cikin yanayi mara daɗi.

Matakin na shiga ƙasashen ba tare da biza ba ya fara aiki nan-take, kuma ana fata zai bunƙasa alaƙar tattalin arziki tsakanin Ghana da Bahamas ta hanyar bunƙasa yawon buɗe ido da tafiye-tafiye tsakanin ƙasashen.

TRT Afrika