Fiye da mutane 300 sun mutu a Sudan saboda ɓarkewar kwalara

Fiye da mutane 300 sun mutu a Sudan saboda ɓarkewar kwalara

Ɓarkewar annobar ta shafi jihohi tara, inda aka ba da rahoton mutane 11,000 sun kamu.
Tsarin kiwon lafiya mara inganci a Sudan da yaƙi ya ɗaiɗaita, ya ƙara dagula ƙoƙarin da ake yi na daƙile cututtuka masu yaɗuwa. / Hoto: Reuters

Adadin wadanda suka mutu sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a Sudan ya kai 348 a cewar ma'aikatar lafiya.

Barkewar cutar ta shafi jihohi tara, inda sama da mutane 11,000 suka kamu da cutar. Bugu da ƙari, ana nuna damuwa game da yiwuwar ɓarkewar zazzabin dengue, bayan mutuwar wasu mutane biyu da ake zargin sun kamu da cutar.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ambaliya sun ta'azzara yaduwar cutar kwalara tun watan Yuni.

Tsarin kiwon lafiya mara inganci a Sudan da yaƙi ya ɗaiɗaita, ya ƙara dagula ƙoƙarin da ake yi na daƙile cututtuka masu yaɗuwa.

Annoba

A watan Agusta Ministan lafiya na Sudan ya ayyana bullar cutar kwalara bayan shafe makwanni ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar da yaki ya daidaita, kamar yadda aka nuna a wani faifan bidiyo da ma'aikatarsa ​​ta fitar.

Haitham Ibrahim ya ce an dauki matakin ne tare da hadin gwiwa da hukumomi a jihar Kassala da ke gabashin kasar, da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, da kwararru bayan "dakin binciken na lafiyar jama'a ya gano kwayar cutar ta kwalara."

Tun a watan Afrilun 2023 ne dai kasar da ke arewa maso gabashin Afirka ke fama da yaki tsakanin sojojin Sudan karkashin shugaban kasar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF), karkashin jagorancin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo.

Rikicin ya haifar da daya daga cikin mafi munin rikicin jin kai a duniya, inda sama da mutane miliyan 25 - sama da rabin al'ummar kasar - ke fuskantar matsananciyar yunwa.

Karancin abinci

An ayyana yanayin yunwa a wani sansanin gudun hijira a babban yankin yammacin Darfur.

Dubban mutane ne suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa, lamarin da ya haifar da karuwar cututtuka da suka hada da gudawa, musamman ga yara.

Kwalara na haifar da zawo mai tsanani da amai da ciwon jiki, kuma galibi tana faruwa ne ta hanyar ci ko shan abinci ko ruwan da ya gurbata da kwayoyin cutar, a cewar hukumar lafiya ta duniya.

Tana iya haifar da rashin ruwa a jiki mai tsanani, wanda zai iya kai wa ga mutuwa a wasu lokuta a cikin 'yan sa'o'i.

TRT Afrika