Ali Lamine Zeine / Photo: Reuters

Firaiminista Ali Mahaman Lamine Zeine ya yi wasu zafafan kalamai a kan alaƙar ƙasarsa da Amurka kan batun yanke dangantakar soji tsakaninsu, a wata hira da ya yi da Washington Post a ranar Talata.

Maline Zeine ya ce Jamhuriyar Nijar ƙarƙashin jagorancin sojojin juyin mulki ta yanke hulɗar soji da Amurka a watan Maris da ya gabata ne saboda ta yi barazanar sanya mata takunkumi.

A tsakiyar watan Maris ne Yamai ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar hadin gwiwa ta soji da ta kulla da Washington, jim kadan bayan da tawagar Amurka ta bar kasar da ke yankin Sahel.

Nijar ta kasance cibiyar yaƙi da ta'addanci a Yammacin Afirka, tare da wani babban sansanin jiragen sama na Amurka kusa da birnin Agadez.

Zeine ya ce mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka a Afirka, Molly Phee, wacce ta jagoranci ziyarar ta tawagar, ta yi barazanar sanya wa birnin Yamai takunkumai idan Nijar ta rattaba hannu kan yarjejeniyar sayar da sinadarin uranium da take haƙowa ga Iran.

'Abin da ba za a yarda da shi ba'

"Na farko, kun zo nan ne don ku yi mana barazana a ƙasarmu, hakan ba abin yarda ba ne," kamar yadda Zeine ya shaida wa Phee.

"Kuma kun zo nan don gaya mana wanda za mu iya yin dangantaka da shi, wanda hakan ma ba za mu amince da tsarin ba. Kuma kun yi hakan ne cikin isa da gadara da rashin girmamawa," in ji Zeine.

A watan Afrilu, Amurka ta amince da janye jami'anta fiye da 1,000 kuma ana ci gaba da tattaunawa da Nijar.

Zeine wanda ya jagoranci tattaunawa da Amurka ya ce “Amurkawa sun zauna a kasarmu ba sa komai a lokacin da ‘yan ta’adda ke kashe mutane da ƙona garuruwa.”

Ƙawance da Rasha

"Ba alamar ƙawance na gari ba ne a zo a cikin ƙasarmu amma a bar 'yan ta'adda su kawo mana hari, mun ga abin da Amurka za ta yi don kare ƙawayenta, saboda mun gani a Ukraine da Isra'ila."

Bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yulin bara da ya hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum, Amurka ta dakatar da tallafin soji.

Saɓanin haka, Rasha da Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun yi maraba da sabbin shugabannin da "hannu biyu", Zeine ya shaida wa Post.

Bayan juyin mulkin, gwamnatin mulkin sojan kasar ta kori sojoji daga kasar da ta yi mata mulkin mallaka wato Faransa, kafin karshen shekara ta 2023 tare da inganta dangantakarta da Rasha, wadda ta aike da malamai da kayan aiki a cikin Afrilu da Mayu.

Sai dai ana shirin ci gaba da tsarin taimakon raya kasa na Amurka da wata sabuwar yarjejeniyar ta kusan dala miliyan 500 cikin shekaru uku, a cewar Ma'aikatar Harkokin wajen Nijar.

AFP