Firaiministan Nijar ya soki kungiyar ECOWAS kan yin "zagon kasa" a yunkurin samun mafita a rikicin kasar bayan wakilanta sun kaurace wa taron da ya kamata su halarta a kasar ranar Alhamis.
"Yau, baya ga Togo da ta yarda ta zo wannan taro, abin takaici shi ne ECOWAS ba ta zo ba," in ji Ali Mahaman Lamine Zeine a wani taron manema labarai da ya gudanar a Yamai, wanda Ministan Harkokin Wajen Togo Robert Dussey ya halarta.
"Akwai masu yin zagon kasa a cikin wannan kungiyar watakila ma har da wasu kasashe da ke cikinta," a cewar Zeine a yayin da Dussey ya ki cewa uffan.
'Rashin adalci ne sanya mana takunkumai'
An tsara taron ne domin Nijar ta tattauna da wakilan ECOWAS kan yadda za a samu mafita game da takunkuman da kungiyar ta kakaba wa kasar bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata.
Sojojin Nijar sun gayyaci wakilan kungiyar zuwa babban birnin kasar amma wakilin Togo ne kawai ya je.
Dussey ya je Yamai a watan jiya inda ya tattauna kan wa'adin mika mulkin kasar ga gwamnatin farar-hula kuma an tsara zai koma kasar tare da sauran wakilan ECOWAS da suka hada da takwaransa na kasar Saliyo Timothy Kabba.
"An sanya wa Nijar takunkumai ne domin a yi mata rashin adalci kuma babu wata doka da ta yarda da hakan. Mun yi bakin kokarinmu domin yin sulhu da su amma abin takaici sun ki amincewa," in ji Zeine.