Daga Abdulwasi'u Hassan
Wata hudu bayan da Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya kaddamar da hakar fetur a Kolmani da ke iyakokin jihohin Bauchi da Gombe a arewa maso gabashin kasar, shugaban kasar ya sake kaddamar da hakar man a karamar hukumar Obi a jihar Nasarawa.
Wannan ya sa an fara hakar man fetur din, wanda shi ne abu mafi daraja da kasar ke da shi, a wurare biyu a arewacin kasar.
Yayin da mutanen yankin ke murna game da fara hako mai a arewacin Nijeriyar, wasu fargaba suke ka da abin da ya faru da yankin Neja Delta mai albarkatun mai, na gurbata muhalli da ayyukan masu fasa bututai, ya faru a arewacin kasar.
Kimanin shekara 66 bayan gano mai a kauyen Oloibiri da ke yankin Neja Delta na kasar a shekarar 1956, har yanzu mutanen yankin suna kokawa kan yadda harkar hakar fetur ke gurbata musu muhalli, "ba tare da sun amfana da arzikin man yadda ya kamata ba."
Hakar mai a jihar Nasarawa
Tun da aka kaddamar da aikin hako mai daga arewa maso gabashin Nijeriyar ne dai ‘yan yankin suka fara murnar cewar wannan wata dama ce ta bunkasa tattalin arzikin yankin da ma kasar baki daya.
Dr Ishaka Shittu Al-Mustapha, malamin jami’a kuma masani kan ma’adinai da ke zaune a birnin Landan, ya shaida wa TRT Afrika cewar: “abun murna ne ga al'ummar yankin don zai iya bunkasa tattalin arzikin mutane a wajen, tare da daidaito a harkar siyasar kasar.”
A kan batun rijiyar man Kolmani da ke jihar Bauchi da Gombe, gwamnatin kasar ta ce an samu hannun jarin da ya kai dala biliyan uku daga ketare.
Shugaban Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC), Mele Kiyari ya ce kamfanin na son sabbin rijiyoyin man da take ganowa su sa man da kasar yake samarwa ya kai ganga miliyan uku a kowace rana.
Ya kara da cewar fetur din da kamfanin ke ganowa a yanzu zai sa iya danyen man da kasar ke da shi a karkashin kasa ya kai ganga biliyan 50 daga ganga biliyan 37.
Ana sa ran cigaba da aikin neman man a wasu fadamu da ke arewacin Nijeriyar.
Da yake kaddamar da hakar fetur din, Shugaba Buhari ya ce lamarin zai kara wadata “ga mutanenmu, kuma ya kara wa kasarmu karfin makamashi.”
Matsalar da aka samu a Neja Delta
Bayan shafe shekaru ana hakar fetur a yankin Neja Delta, mutanen wurin suka fara kokawa kan rashin amfana da alherin man da ake hakowa daga yankin nasu.
“Amma samun mai ka iya zama alkhairi ko sharri,” in ji Suraj Oyewole, wani mai sharhi kan harkar makamashi.
Kama daga lokacin da aka kafa kungiyar MOSOP mai fafatukar kare hakkin ‘yan garin Ogoni a shekarar 1992, har zuwa yau an yi ta samun tashin hankali wanda ke jawo asarar rayuka.
A wasu lokutan kuma a kan sace mutane musamman ma'aikatan kamfanonin kasashen waje da ke ayyukan hakar mai a yankin.
Kazalika al'ummomin wajen suna yawan korafe-korafe na gurbata musu muhalli ko kuma rashin bai wa ‘yan yankin abin da ya dace cikin arzikin man da ake samu a wajen.
Duk da cewa gwamnatin marigayi Umaru Musa ‘Yar adua ta kirkiri shirin yin afuwa ga masu tayar da kayar baya na yankin a 2009 don samun zaman lafiya mai dorewa, gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan da ta Shugaba Buhari mai ci a yanzu ma sun yi ta fama da matsalar fasa bututan ma.
'Yan bindigan yankin da ke wannan barna kan yi ikirarin cewar suna fafutukar ganin sun amfana daga arzikin da ake samu a yankinsu ne.
Ban da wannan, masunta a yankin na Neja Delta suna kokarin neman a biya su diyya game da yadda mai ke gurbata ruwa tare da kashe kifaye, lamarin da ke yin illa ga sana'ar da suka dogara da ita don samun rufin asiri.
A shekarun 2008 da 2009, yoyon danyen mai da ya gurbata ruwa ya sa masunta a garin Bodo da ke karamar hukumar Gokana a jihar Ribas sun kai kamfanin fetur na Shell a kotu.
Daga bayan kamfanin ya amince cewar zai biya su diyyar dala miliyan 83.5. Manoma da masu fafatukar kare muhalli da yawa sun bi wannan sahun.
Ta yaya mutanen arewacin Nijeriya za su kauce wa matsalar da aka samu a Neja Delta?
Mai sharhi kan ma'adinai Dr Ishaka Shittu ya ce ya kamata ya yi a dinga juya kudin man ta hanyar yin kasuwanci da shi, amma ta salon da al'ummar yankunan da ke da arzikin fetur din za su aminta da shi.
"Kamata ya yi a dinga bai wa kamfanonin zuba jari na kasa da kasa kudin man domin juyawa da kuma kula da shi,” masanin ya ce.
Ya ce irin wannan kamfanin zuba jarin zai tabbatar cewar an saka kudin mai din a inda ‘yan garin suka fi bukata.
Suraj Oyewole ya ce ya kamata mutanen da aka samu fetur a wurarensu su mayar da hankali kan kare muhallinsu daga matsalar yoyon danyen mai.
Ya kara da cewar ya kamata mutane su guji sakalcin da ka iya sa su kin aiki saboda tunanin cewa an samu arzikin mai a garinsu.
Yaya mutanen yankin za su amfana da fetur din?
Gwamnan jihar Nasarawa, inda aka fara hakar mai a baya-bayan nan, Abdullahi Sule ya ce yana da yakinin cewa fetur din da aka fara haka a jiharsa zai taimaka wa mutanen jihar.
“Da muka isa rijiyar fetur dina a yau, abin da ya faranta mini rai matuka shi ne yadda na ga matasa daga jihar Nasara ne suke kan injin hakar man, wato har an riga na ba su aiki,” in ji gwamnan a hirar da ya yi da gidan talabijin din Channels.
Ya ce matasan za su samu kwarewa baya ga samun aiki daga man da aka samu a jihar.
Dr Ishaka Shitu Al-Mustapha ya ce dokar mai ta Nijeriya ta ba da damar ware kashi uku na arzikin fetur din da ake samu ga al’ummar da ke zama a inda ake hako man.
Ya ce ya kamata a rinka amfani da kudaden wajen samar da abubuwan more rayuwa ga mutanen garuruwan da ake hako man.
“Abin da ya kamata arewacin Nijeriya ta yi shi ne ta sa mutanen da ake hako mai a wurarensu su kafa kwamitin amittattu da za su rinka kula da yadda ake sarrafa kudin,” in ji Dr Ishaka.