Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Bauchi ta ce ta soma gudanar da bincike kan wata mata da ake zargi da kashe mijinta a Bauchi.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Aminu Gimba Ahmed ya fitar, lamarin ya faru ne a Unguwar Kofar Dumi inda wata mata mai mai suna Maimuna ‘yar shekara 21 ta caka wa mijinta wuka.
Rundunar ta ce bayan ta samu kiran gaggawa kan lamarin, nan take jami’anta suka je suka kama matar wadda ake zargi da kashe mijinita.
“Bayan samun bayanai, jami’an tsaro cikin gaggawa suka je inda lamarin ya faru inda suka dauki wanda aka caka wa wuka da wadda ake zargi zuwa Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi domin duba lafiyarsu.
“Rahotannin da aka samu daga likitoci sun tabbatar da cewa mutumin ya rasu sakamakon raunin da ya samu a kirjinsa sa’annan wadda ake zargi ta samu dan rauni a cikinta,” in ji sanarwar.
“Binciken wucin gadi ya nuna cewa wadda ake zargi (Maimuna Suleiman) ta caka wa mijinta Aliyu Mohammad bayan rashin jituwa da suka samu a ranar 5 ga watan Yulin 2023, da misalin 6:00 na yamma a gidansu na aure.”
Rundunar ‘yan sandan ta ce a lokacin da ake yi wa wadda ake zargi tambayoyi, ta amsa laifin da ake zarginta da shi.
Haka kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Auwal Musa Mohammad ya bayar da umarnin mayar da binciken Sashen Binciken Manyan Laifuka SCID, domin ci gaba da bincike.
Haka kuma sanarwar ta ce da zarar an kammala binciken za a tura wadda ake zargi da aikata kisan zuwa kotu.