Faransa ta sanar da rufe ofishin jakadancinta da ke Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar a ranar Alhamis.
Kamfanin dillancin labarai na Actu Niger ya rawaito cewa, a wata wasika da ya aike wa dukkan ma’aikatansu, jakadan Faransa a Nijar, Sylvain Itté ya sanar da su cewa Ma’aikatar Turai da Harkokin Wajen Faransa ta dauki matakin rufe ofishin jakadancinsu da ke Yamai na ‘wani lokaci ba mai tsawo ba’.
Jakadan, wanda shugabannin sojin Nijar suka kora daga kasar ya ce wannan mataki ya biyo bayan yadda ofishin jakadancin Faransa a kasar ya gaza gudanar da cikakken aikinsa na diflomasiyya da ya rataya a wuyansa tun bayan juyin mulkin watan Yuli.
Sanarwar ta kuma ce an sallami dukkan ma’aikatan ofishin, kuma za a biya su hakkokinsu.
Jakada Sylvain Itté ya ce “Tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga Yulin 2023 da harin da aka kai wa ofishinsu a ranar 30 ga Yuli, 2023, ofishin jakadancin Faransa ya gaza gudanar da ayyukan diflomasiyya da suka rataya a wuyansa, sakamakon dokokin matsi da mahukuntan Nijar suka sanya musu.
"Duk da bukatar da aka miƙa musu, mahukuntan na Nijar sun ƙi sakarwa ofishin mara ya gudanar da ayyukansa cikin yanayi mai kyau.”
Wannan mataki bai zo da mamaki ba duba da rikicin diflomasiyya da ya barke tsakanin Yamai da Paris tun bayan juyin mulkin 26 ga Yulu, 2023, inda sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
Bayan soke yarjejeniyar ayyukan soji da Faransa, gwamnatin sojin ta Nijar ta kuma bayyana cewa ba a bukatar jakadan Faransa Sylvain Itté a kasar, daga baya kuma aka fitar da sanarwar korar sa daga kasar.
Sabuwar gwamnatin sojin ta kuma bukaci da sojojin Faransa su tattara nasu su bar kasar.