Babban dalilin da ya jawo rashin jituwar shi ne kan batun mayar da rundunar RSF cikin sojojin kasar / Hoto: AA

An shafe makonni ana cikin fargaba sakamakon tsamar da ke tsakanin Janar-janar biyu mafi karfi a Sudan, watanni 18 bayan sun hada kansu sun yi juyin mulki, lamarin da ya sa kasar ta kauce daga hanyar da aka dauka ta mayar da mulki ga farar hula.

Rikicin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar nan mai karfi ta RSF ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 100 farar hula, inda daruruwan jama’a kuma suka samu raunuka.

Rikicin da ake yi a halin yanzu tsakanin shugaban sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma shugaban rundunar Rapid Support Forces ta RSF, Janar Mohammed Hamdan Dagalo, ya kara kazanta ne a ranar Asabar kan batun iko da kasar mai albarkatun kasa kuma mai mutum sama da miliyan 46.

Hankoron da suke yi na kan mulki ya jefa kasar cikin rikici, a Khartoum babban birnin kasar da sauran biranen da ke kusa da ke cikin Sudan, inda ake jin karararrakin fashewa masu karfi, da harin sama da na makaman atilari da musayar wuta mai karfi a unguwanni masu dumbin jama’a.

Duka janarorin biyu wadanda dukansu suke da gomman dakaru a birnin Khartoum, sun lashin takobin cewa ba za su tattauna ba kan yarjejeniyar tsagaita wuta duk da matsin lambar da ake fuskanta daga kasashe ketare.

Shugaban sojin Sudan al-Burhan da kuma Hamdan Dagalo wanda aka fi sani da Hemeti, dukansu na zargin juna da fara tsokano rikicin, kuma dukansu suna ikirarin iko da wasu wurare.

Yadda adawa ta koma rikici

A watan Oktoban 2021, Burhan da Dagolo sun shirya juyin mulki, lamarin da ya jawo koma baya ga mika mulki zuwa ga farar hula tun bayan juyin mulkin da aka yi a 2019 inda aka hambarar da gwamnatin Omar al Bashir.

Sojojin kasar da RSF sun sa hannu kan wata yarjejeniya a Disamba, sai dai an kasa cimma matsaya kan yarjejeniya ta karshe sakamakon zaman doya da manja da ake yi tsakanin bangarorin biyu.

Babban dalilin da ya jawo rashin jituwar shi ne kan batun mayar da rundunar RSF cikin sojojin kasar, wadanda za su rinka iko kan mayakan da kuma makamansu.

Burhan, wanda soja ne da ya fito daga arewacin Sudan kuma ya rinka samun karin girma a karkashin mulkin Bashir wanda yanzu haka yake a gidan yari, shi ne ya karbi mulkin kasar.

Sai kuma Dagalo wanda ya fito daga yankin Darfur da ake yawan kiwon rakuma, shi ne ya zama mataimakinsa.

Sai dai wannan “aure ne na bukata” kamar yadda wani mai bincike mai zaman kansa kuma mai sharhi kan tsare-tsare Hamid Khalafallah ya bayyana.

Rikicin da ke tsakanin janarorin biyu ya kara kamari a daidai lokacin da Hemeti ya fito ya bayyana juyin mulkin a matsayin “kuskure” wanda ya kasa kawo sauyi inda ya ce ya kara karfafa sauran burbushin mulkin Bashir.

Wani darakta a Kungiyar Warware Rikici ta Kasa da Kasa ta yankin Kusurwar Afirka, Alan Boswell, ya ce a cikin yarjejeniyar, Dagalo ya ga wata dama da zai samu cin gashin kai daga sojin, tare da cimma “buruka na siyasa.”

Sai dai, wannan batun mika mulkin ya jawo gagarumin rikici a tsakanin Burhan da Hemeti inda aka kare da yin fito na fito da gwada kwanji maimakon zazzafar muhawara a teburin sasantawa, kamar yadda Kholood Khair, wacce ta kirkiri kungiyar bincike ta Confluence Advisory mai cibiya a Khartoum ta ce.

Mece ce RSF?

An kafa RSF a 2013 karkashin jagorancin Janar Dagalo kuma ta samo asali ne daga mayakan sa-kai na Janjaweed da suka fafata da 'yan tawayen yankin Darfur.

Tun daga wancan lokacin, Janar Dagalo ya gina runduna mai matukar karfin fada a ji wadda masana suka ce tana da dakaru kusan 100,000.

Rundunar ta fafata a yake-yake da dama ciki har da na Yemen da Libya.

An zargi rundunar RSF da hannu wajen take hakkin dan adam, ciki har da kisan-gillar da aka yi wa masu zanga-zanga fiye da 120 a watan Yunin 2019.

Kawancen rundunar soji karkashin Janar Burhan da rundunar RSF da ke karkashin Dagalo ne ya kifar da gwamnatin Omar al-Bashir a 2019.

Daga nan ne suka kafa gwamnati ta hadin gwiwa tsakanin farar hula da soji.

Babakeren kasashen waje

A lokacin mulkin Omar al Bashir, Rasha ce ta fi karfin iko a Sudan, bisa yarjejeniyar gina sansanin sojin ruwa a gabar Tekun Maliya da ke kasar.

Bayan hambarar da Bashir, Amurka da kasashen Turai suka fara gasa da Rasha don samun iko a Sudan, wacce ke da dumbin arzikin kasa da suka hada da zinare, amma kuma yaki da rikice-rikice da juyin mulki sun yi mata katutu.

Kazalika rundunar sojojin haya na kamfanin Wagner na Rasha ya samu wajen zama a kasar.

Gwamnatin mulkin soji ta Sudan da rundunar RSF suna da kyakkyawar alaka da Saudiyya da UAE, kuma sun shiga cikin rundunar kawance da Saudiyya ta jagoranta a yakin Yemen.

Sojoji ne ke juya akalar mafi yawancin tattalin arzikin kasa, yayin da RSF ke da iko da manyan yankunan hakar zinare, fanni mafi muhimmanci na samun kudaden shiga.

Masar ma tana da alaka ta kut da kut da sojojin Sudan.

Masu sharhi na ganin Dagalo na kokarin bata martabar rundunarsa ne, wadda ta faro a matsayin kungiyar ‘yan tawaye da ta aikata munanan abubuwa a lokacin rikicin Darfur.

Mene ne abu na gaba?

A cewar kwararru, rikici tsakanin janar-janar din biyu na faruwa ne a kan neman mulki da iko, kuma dukkansu suna kallon fadan a matsayin wanda bangare daya zai yi nasara a kan dayan.

Ci gaba da fadan nasu a kan titi na nufin ci gaba da kashe fararen hula, kuma hakan zai yi wa dukkanninsu wahalar iya mulki a cikin wannan yanayi.

Boswel ya ce “dukkan bangarorin biyu suna da yakinin cewa kowane yaki zai jawo musu abubuwa da yawa, da kashe-kashe da kuma dadewa ana yi, kuma ko da wani bangare ya samu yin nasara a Khartoum, to za a ci gaba da yakin a wasu sassan kasar.

TRT World