A yayin da gwamnatoci a Nijeriya ke kokarin yaki da cututtuka masu yaduwa, su kuwa hukumomi a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya na ta fafutukar ganin sun dakile yaduwar cutar tarin fuka da ake samun karuwar masu dauke da ita a jihar.
A baya-bayan nan kawai an samu kusan mutum 300 da suka kamu da cutar a Jihar Kano, wacce tana daya daga cikin jihohi biyar na Nijeriya da cutar ta fi yawa a cikinsu, inda ake da mutum 34,547 masu ita.
A makon jiya ne Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta fara gudanar da aikin tantance mutane don gano masu dauke da cutar tarin fukar.
A yayin tattaunawa ta wayar tarho da TRT Afirka Hausa, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa sun baza ma’aikatansu zuwa dukkan kananan hukumomin jihar 44, da asibitoci da gidajen gyaran hali da manyan makarantun gaba da sakandire don tantance mutane.
“A halin yanzu a cikin kwana takwas na tantancewar da muka fara, an tantance mutum 41,056, kuma daga cikin su an samu mutum 238 dauke da cutar tarin fuka.
Kwamishinan ya ce daga cikin wannan adadi 44 yara ne kanana, kuma tuni an fara bai wa wadanda aka gano dauke da cutar magani.
“Sannan mun saka mutum 305 a kan magani na kariya wadanda su ba cutar ce da su ba, amma saboda suna da kusanci da masu dauke da cutar, dole sai an ba su kariya domin gudun kar su kamu da wannan cuta,” in ji Dr. Yusuf.
Kokarin gwamnati na yaki da yaduwar cutar
Matakan da gwamnatin jihar Kano ta dauka don yaki da ci gaba da bazuwar cutar sun hada da wayar da kan al’umma kan alamominta da matakan kauce mata.
Kwamishinan Lafiyar ya ce “Muna fadakar da al’umma don su san ta yadda ake gane cutar; duk zazzabi ko tari da suka wuce sati biyu duk da ana shan magani, ko mutum ya dinga ramewa, da kuma yawan gumi da daddare, to da zarar an ga wadannan alamomi a je wajen tantancewa.
“Sannan wannan tantancewa kyauta ce, maganinta kyauta ne, kuma ba a fara shan maganin a dakata, sai an yi wata shida ana sha,” in ji shi.
Hukumomin Jihar Kano sun ce mataki na biyu shi ne tantancewar, ita kanta tantancewar tana hana cutar yaduwa.
“Duk mutumin da aka tantance aka gano yana da cutar, to za a bai wa mutum maganin da zai warkar da shi. Hakan zai hana cutar yaduwa,” in ji Dr Yusuf.
Rawar da sauran shugabanni za su taka a yaki da tarin fuka
Baya ga bangaren gwamnati, sauran shugabannin al’umma musamman ma na gargajiya na da muhimmiyar rawar takawa wajen yaki da yaduwar wannan cuta.
Dr. Yusuf ya ce “Shugabanni kamar masarautu na da gudunmowar takawa wajen fadakarwa da wayar da kan jama’a kan su fahimci mene ne wannan ciwo.
“Wannan zai taimaka al’umma su shiga ciki. Su saki jiki su gane cewa ga iyayen gari ma sun karbe shi.”
Kira ga al’umma
Kwamishinan na Lafiya na jihar Kano ya kuma yi kira ga al’umma da su kai duk wanda ake ganin na dauke da alamun cutar zuwa wajen tantancewa.
Sannan idan aka tabbatar da yana dauke da cutar, to a tabbatar da ya karbi magani, kuma ya yi amfani da shi yadda likita ya umarta.
Ya kara da cewa “Kiran da za a yi ga al’umma shi ne da zarar an ga mai dauke da tarin fuka a kai shi asibiti a tantance shi.
Kuma idan yana da shi, a tabbatar ba a tsangwame shi ba, a tabbatar ya sha wannan magani har na wata shida kamar yadda likita ya yi umarni.”
Mene ne tarin fuka?
Cutar Tarin Fuka da aka fi sani da TB mummunar cuta ce da ke shafar huhu sakamakon yaduwar kwayoyin cutar bakteriya. Cutar na bazuwa ta iska idan masu dauke da ita suka yi tari ko atishawa ko suka tofar da yawu.
Ana iya daukar matakan kariya daga cutar kuma ana iya warkewa baki daya.
Alamomin cutar sun hada da:
- Tari na tsawon lokaci (wani sa'in ma ar da jini)
- ciwon kirji
- kasala
- yawan gajiya
- ramewa
- zazzabi
- gumi cikin dare.
Matakan dakile ta da hana yaduwarta
- A je a ga likita idan ana fama da zazzabi da tari masu naci da ba sa jin magani ko rama ta ba gaira ba dalili
- Idan ka san kana cikin hadarin kamuwa da cutar to ka tabbatar ka yi gwaji, misali idan kana da cutar HIV ko kuma ka yi mu'amala da mai TB
- Ka tabbatar ka shanye dukkan maganin cutar da aka ba ka a asibiti
- Kar a dinga yin tari ko atishawa a cikin mutane ba tare da an kare da kyalle ba, ta hanyar rufe baki da hanci
- Ana iya yi wa yara rigakafin cutar a lokacin da suke jarirai.
Yawan masu cutar a duniya
- A shekarar 2021, an kiyasta cewa mutum miliyan 10.6 ne suka kamu da cutar tarin fuka a fadin duniya
- Mutum miliyan shida maza ne, miliyan 3.4 mata ne sai kuma miliyan 1.2 yara
- Kusan kowace kasa ta duniya akwai masu fama da cutar
- A 2021, kasa takwas ne ke dauke da fiye da kashi biyu cikin uku na yawan masu cutar kamar haka; Indiya (28%), Indonesiya (9.2%), China (7.4%), Philippines (7.0%), Pakistan (5.8%), Nijeriya (4.4%), Bangladesh (3.6%) da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo (2.9%).