Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Abdourahamane Tiani/ Hoto: Presidence du Niger/ X

Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) za ta kawo kammala aikin haɗin gwiwa na soji wanda ya ƙunshi sojoji da dama a Nijar a ƙarshen watan Yuni, a cewar wata sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, tana mai kafa hujja da yanayin siyasar ƙasar da ke ƙarƙashin mulkin soji.

Har zuwa lokacin da aka yi juyin mulki a Nijar a shekarar 2023, ƙasar na ɗaya daga cikin ƙawayen kungiyar Tarayyar Turai a yankin Sahel inda ake yaƙi da masu tayar da ƙayar baya da suka kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da matsugunansu.

A ɓangare guda kuma, shugabannin mulkin sojin ƙasar sun yi matuƙar matsa wa Faransa wacce ta yi wa Nijar mulkin mallaka har sai da ta janye dakarunta.

Haka kuma sun yanke hulɗar soji da Amurka wadda suka bai wa umarni ta kwashe sojojinta daga ƙasar, yayin da a gefe guda suka ƙarfafa alaƙa da Rasha.

''A yau Majalisar EU ta yanke shawarar ƙin tsawaita wa'adin shirin haɗin gwiwar soji da Nijar mai suna (EUMPM) daga ranar 30 ga watan Yunin 2024, la'akari da yanayin siyasar da ƙasar ke ciki," in ji sanarwar da ta fitar.

A shekarar 2022 ne aka soma aikin haɗin gwiwar a ɗaya daga cikin ƙasashe mafi fama da talauci a duniya inda aka jibge dakarun sojin Turai 50 zuwa 100 don su taimaka wajen samar da tsaro da ci gaba.

AFP