Kwanan nan ne hukumar EFCC ta yi shelar korar jami'anta 27 bisa laifin almundahana: Hoto/Facebook/EFCC

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Nijeriya ta’annati (EFCC) ta ce ta tsare jami’anta 10 kan zargin satar kayayyakin aiki inda suka kasa bayanin yadda aka yi da su.

A wata sanarwar da ya fitar ranar Laraba, shugaban sashen watsa labaran EFCC, Dele Oyewale, ya ce kamun da aka yi wa jami’an ya biyo bayan umarnin da shugaban hukumar ta EFCC, Ola Olukoyede ya bayar ne.

Duk da cewa sanarwa da hukumar ta fitar ba ta ambaci abubuwan da suka sata ba, rahotanni daga Nijeriya sun nuna cewa jami’an sun fasa ɗakin adana kayayyakin shaida ne inda suka saci takardun kuɗi na ƙasashen waje da kuma zinari.

Wannan na faruwa ne kwanaki bayan hukumar EFCC ta yi shelar korar jami’anta 27 bayan an same su da hannu a aikata almundahana.

A sanarwar, mai magana da yawun hukumar EFCC ya ce kama jami’an kan zargin satar abubuwa “wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi na daƙile cin hanci da rashawa a hukumar EFCC.”

“A halin yanzu jami’ai goma na babban ofishin yanki na hukumar da ke Legas ne aka tsare game da binciken da ake kan wasu abubuwan da suka ɓace ta hannunsu,” in ji sanarwar.

“Waɗannan jami’an, waɗanda aka kama a makon da ya gabata bisa umurnin shugaban hukumar, Mr. Ola Olukoyede, ana musu tambayoyi game da satar abubuwan da ba su iya bayanin inda suke ba.

“Masu bincike na samun gagarumar nasara, kuma waɗanda aka samu da laifi za su fuskanci matakan ladabtarwa na cikin hukumar,” a cewar Oyewale.

TRT Afrika da abokan hulda