Baya ga kuɗi da aka miƙa ga ‘yan ƙasashen na Amurka da Sifaniya da Switzerland, akwai motoci da gidaje da aka ƙara musu da su. / Hoto: EFCC

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta ce ta mika kudaden da suka kai dalar Amurka $132,362.43 da kuma naira N78,566,324.81 ga wasu Amurkawa, da Sifaniyawa da ‘yan Switzerland waɗanda ‘yan damfara na cikin gida suka zalunta.

Hukumar ta bayyana matakin a matsayin wata alama ta jajircewarta na magance yi wa tattalin arziƙi ta’annati tare da mayar wa waɗanda aka zalunta haƙƙinsu.

A cewar wata sanarwa da hukumar ta EFCC ta fitar, shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ne ya mika kuɗaɗen a ranar Juma’a a hedikwatar hukumar da ke Jabi, Abuja.

Baya ga kuɗi da aka miƙa ga ‘yan ƙasashen na Amurka da Sifaniya da Switzerland, akwai motoci da gidaje da aka ƙara musu da su.

Jakadar Sifaniya a Nijeriya Maria Higon, ta karɓi shaidar dala 1,300 da kuma naira miliyan 30 wanda aka aika ga ofishin jakadancin Sifaniya a Nijeriya domin mayar wa Maria Del Rosario San Jose wadda aka zalunta.

Florent Geel, Babban Jami'in Harkokin Siyasa, Sakatare na Farko na Ofishin Jakadancin Switzerland ya karbi $ 100,011.43 a madadin wanda aka zalunta, Chantai Helene Lavancy, wanda aka fi sani da Chantai Helene Maeder.

Charles Smith, wanda ma’aikacin hukumar FBI ne a Amurka ya karɓi dala $7,344 da naira N7,963,483.35 sai kuma Bitcoin a da darajarta ta kai dala 4,470 amadadin Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya don kaiwa ga wanda abin ya shafa, Maria Jesus Brockell.

TRT Afrika