EFCC

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Nijeriya zagon ƙasa wato EFCC ta yi Allah wadai da masu amfani da kayanta suna haɗa bidiyon barkwanci.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta a ranar Litinin, hukumar ta nuna matuƙar damuwa dangane da yadda wasu masu wasan barkwanci ke amfani da kayan aikin hukumar waɗanda suka haɗa da riguna domin yin wasan barkwanci inda ta ce hakan na zubar da kimar hukumar.

Sanarwar da hukumar ta EFCC ta fitar na zuwa ne bayan wani tsohon bidiyon barkwanci mai suna “EFCC and Army Wahala” ya ƙara yawo a shafukan sada zumunta.

“Wani tsohon bidiyo mai suna: “EFCC and Army Wahala” na ƙara samun karɓuwa a kafafen sada zumunta. Wannan ne ya ja EFCC ke ƙara jaddada gargaɗinta ga masu haɗa bidiyo da sauran masu amfani da shafukan sada zumunta kan su guji amfani da kayanta ba bisa ƙa’ida ba.

“EFCC and Army Wahala” wasan kwaikwayo ne kan yadda EFCC ke gudanar da ayyukanta. Abin kunya ne yadda aka nuna wasu da ake cewa jami’an hukumar ne a bidiyon suna ta’addanci kan ‘wadanda ake zargi, hakan ba wai abin kunya ne kaɗai ba amma alama ce ta yadda ake so a goga wa EFCC ɗin kashin kaji,” in ji sanarwar.

“Jami’an EFCC ba azzalumai bane. An horar da su a matsayin jami’ai na zamani waɗanda ke da tarbiyya, sanin haƙƙin farar hula da kuma ganin girman jama’a, daga ciki har da waɗanda ake zargi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

TRT Afrika