"Ba za a amince da shekaru na mika mulki ga farar hula ba", in ji Abdel-Fatau Musah, kwamishinan harkokin siyasa na ECOWAS yayin tattauna da Aljazeera. Hoto: AP

Kasashen Yammacin Afirka sun yi watsi da kiran da shugabannin juyin mulki na Nijar suka yi na daukar wa'adin shekaru uku kafin su mika mulki ga farar-hula a kasar, a yayin da ECOWAS ke duba yiwuwar daukar matakin soji kan kasar.

Janaral Abdourahamane Tchiani ya bayyana cewa sai nan da shekara uku za su mayar da mulki ga farar-hula bayan da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan jiya.

Wannan sanarwa da ya bayar ta zo ne bayan da wakilan kungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka da ta yi barazanar amfani da karfi don mayar da Bazoum kan mulki, suka ziyarci Nijar kan daukar matakin diflomasiyya na karshe kan lamarin.

"Ba za a amince da shekaru na mika mulki ga farar hula ba", in ji Abdel-Fatau Musah, kwamishinan harkokin siyasa na ECOWAS yayin tattauna da Aljazeera.

"Muna son a dawo da aiki da kundin tsarin mulki nan da nan,"

Babu 'wasan yara'

A wani sako da ya fitar ta tashar talabijin a ranar Asabar, Janar Tchiani ya zargi ECOWAS da shirin kai wa Nijar hari, ta hanyar hada runduna ta musamman tare da goyon bayan dakarun kasashen waje, amma bai bayyana wacce kasa ba ce.

Ya ce "Idan za a kai mana wani hari, ba zai zama wasan yara ba, ya kamata wasu mutane su yi tunani."

Shugabannin ECOWAS sun bayyana dole ne su shirya a yanzu haka saboda Nijar ce kasa ta hudu a Yammacin Afirka da aka samu juyin mulkin soji tun 2020 zuwa yau, bayan kasashen Burkina Faso da Guinea da Mali.

Labari mai alaka: Katse wutar lantarki a Nijar ya sa amfani da janareto

Kungiyar ta amince da shirya 'dakarun kar-ta-kwana' a matsayin matakin karshe na dawo da dimokuradiyya a Nijar.

Kungiyar ta bayyana cewa a shirye take ta dauki mataki, duk da tana bin hanyoyin diflomasiyya, kuma ba ta bayyana yaushe za a dauki matakin sojin ba.

Goyon bayan juyin mulki

Ba kamar ayyukan ECOWAS a farkon watan Agusta ba, a wannan lokacin tawagar ta gana da Tchiani da kuma Bazoum, wanda ake tsare da shi da iyalinsa a fadar shugaban kasa, kuma yana iya fuskantar laifukan cin amanar kasa.

Hotunan da aka gani a tashar talabijin ta Nijar sun nuna Bazoum na murmushi yana gaisa wa da mambobin tawagar.

A ranar Lahadi, dubban 'yan Nijar sun fita zanga-zanga a babban birnin kasar don nuna goyon baya ga juyin mulkin.

Sabbin shugabannin soji na asar ta yankin Sahel sun haramta zanga-zanga a hukumance, amma kuma ana baiwa masu goyon bayan juyin mulkin izinin yin hakan.

A birnin Agadez na arewacin Nijar, daruruwan masu zanga-zanga ne suka nemi fitar sansanonin sojin kasashen waje daga Nijar, da suka hada da na Amurka da ke filin tashi da saukar jiragen saman garin.

Amurka na da kusan sojoji dubu daya a Nijar, inda Faransa kuma ke da kusan 1,500 da suke yaki da kungiyoyin jihadi.

Yankin Sahel na gwagwarmaya da kungiyoyin ta'adda da ke da alaka da Alqa'eda da IS da kuma shugabannin juyin mulki a yankin na bayyana dalilan tabarbarewar tsaro ne ke sanya su kwace mulki.

Yara 'na cikin tsananin bukata'

Rikicin Nijar na ta'azara atsarin da miliyoyin yara masu rauni ke ciki a kasar, in ji hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya, inda ta kara da cewa "babbar matsalar jin kai ga wadda ake da ita".

Wakilin UNICEF a Nijar Stefano Savi ya bayyana cewa "Sama da yara kanana miliyan biyu rikicin ya shafa, kuma suna cikin tsananin bukatar taimakon jin kai."

A wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, ya ce tun ma kafin wannan rikicin, an yi hasashen akwai yara kusan miliyan 1.5 'yan kasa da shekaru biyar da ke fuskantar karancin cimaka a 2023 a kasar.

Kasar ta yankin Sahel da ba ta da iyaka da teku, na daya daga cikin kasashen duniya mafiya rauni da talauci, kusan ko yaushe tana can kasa a jerin alkaluman Ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya.

UNICEF ta bayyana cewa akwai damuwa sosai game da rasa lantarki a kasar, wanda na da matukar muhimmanci don adana alluran riga-kafin yara kanana da sauran kayan aiki.

Haka zalika kungiyar ta bayyana damuwa kan wasu kayan kubutar da rayuka a cikin kwantenoni 21 da suka makale a kan iyaka da ke tashar jiragen ruwan Kwatano.

Akwai wasu kwantenoni 29 na Nijar dauke da kayan agajin gaggawa, abinci da sirinji da ke kan teku.

AFP