Shugaba Buharin zai kaddamar da ayyuka 14 a fadin kasar /Hoto: Presidency

Makon gobe ne zai kasance na karshe a mulkin Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari bayan shafe shekara takwas a kan mulki, inda zai mika mulki ga sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Sai dai duk da cewa 'yan kwanaki ne suka rage masa a kan mulki, Shugaba Buhari ya shirya kaddamar da wasu jerin ayyuka 14 kafin ya mika mulkin a farkon mako mai zuwa.

Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafofin sada zumunta na zamani, Bashir Ahmad ne ya bayyana jerin ayyukan da shugaban kasar zai kaddamar a wannan makon, a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

Ayyukan da za a kaddamar su ne:

  • Matatar Mai ta Dangote da ke Legas
  • Gadar Loko zuwa Oweto da ke jihar Nasarawa
  • Gadar Second Niger Bridge da ta hada jihohin Delta da Anambra
  • Gadar Ikom a jihar Cross River
  • Hanyar Kaduna zuwa Kano (wani bangare na aikin titin Abuja zuwa Kano)
  • Sakatariyar Tarayya a jihar Zamfara
  • Sakatariyar Tarayya a jihar Anambra
  • Sakatariyar Tarayya a jihar Bayelsa
  • Wurin hada taragon jirgin kasa a jihar Ogun
  • Cibiyar nazarin ayyukan majalisa da dimokradiyya ta kasa a Abuja
  • Sabon wurin saukar fasinjoji a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a jihar Kano
  • Wasu ayyuka a Kwalejin Koyon Tukin Jirgin Saman a Zaria
  • Filin jirgin saman jihar Ebonyi a Ebonyi
  • Sabuwar hedikwatar hukumar kwastam din kasar a Abuja.

Me ya sa shugaban ke kaddamar da ayyukan dab da saukarsa?

Wannan ita ce tambayar da watakila mutane da dama suke yi wa kansu.

TRT Afrika ta tuntubi wani masanin harkokin siyasa a Jami'ar Abuja, Dr Abubakar Kari, wanda ya ce wannan ba sabon abu ba ne ga shugabannin da ke shirin barin gado.

"A duk lokacin da wa'adin wata gwamnati ya karato ko ya zo karshe, to za ta yi kokarin ta tabbatar da cewa ta fada wa duniya cewa ayyuka kaza da kaza da wannan da wancan a lokacinta aka yi.

"Za ka ga ana ta hanzarin kaddamar da ayyukan da aka faro wasunsu ma ko ba a karasa su ba," in ji shi.

Ya kara da cewa: "Kawai suna so ne tarihi ya tuna cewa su ne suka fara wannan aiki ko su ne suka kammala shi.

"Saboda a tunaninsu idan ba su yi haka ba, wadanda suka zo bayansu, ko dai za su yi ikirarin cewa su ne suka yi aikin ko kuma ba za su fada wa duniya sunan ainihin wanda ya yi aikin ba."

Su ma 'yan Nijeriya ba a bar su a baya ba wajen tofa tasu kan wannan lamari, inda suka dinga yin tsokaci a kasan sakonni da Bashir Ahmad ya wallafa.

Sai dai a yayin da wasu ke yabo da jinjina, wasu kushe suka dinga yi kan wannan labari.

Salihu Tanko @salihutanko11 ya ce: "Ba a taba ganin irin wannan ba a tarihin Nijeriya, tarihi ba zai manta da Shugaba Buhari ba saboda manyan ayyukan ci gaba da ya yi. Na jinjina maka."

Shi kuwa Dammy @oyeladedami cewa ya yi: "Ya kaddamar da ayyukan da suka fara aiki nan take, amma ba ayyukan bogi ba, kamar tashar Baro."

"Ya kasa gina matatar mai a tsawon shekara takwas. Yanzu ya kaddamar da Matatar Man Dangote. Wai shin ba ku ji kunya ba," in ji IGWE @igwe_manuel.

SAAD @mahmudchiroma yaba wa shugaban ya yi, inda ya ce: "Shugaban da ba a taba samun irinsa ba… Gwarzo, uban sabuwar Najeriya…kowa ya kamata ya jinjina maka."

A karshe akwai ra'ayin Ahmad N.M @ahmadrufai wanda shi ya kalubalanci Bashir Ahmad ne, inda ya ce masa "Me ya sa ba ka saka har da shirin dawo da kamfanin sufurin jirgin saman Nigeria Airways ba?"

TRT Afrika