Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika ECOWAS ta umarci dakarunta su sanya damar yaki da sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar.
ECOWAS ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar ranar Alhamis bayan kammala taronta a Abuja, babban birnin Nijeriya.
Sai dai shugabanta Bola Ahmed Tinubu ya ce har yanzu akwai yiwuwar sulhu da sojojin kuma amfani da karfin soja shi ne zai kasance "mataki na karshe" na warware halin da ake ciki a Nijar.
ECOWAS ta ce sojojin da suka kwace mulki a Nijar "sun yi fatali" da dukkan hanyoyin diflomasiyya da ta bi na yin sulhu da su game da rikicin.
Don haka ne kungiyar ta "bayar da umarni ga dukkan Manyan Hafsoshin Tsaro su yi gaggawar daura damarar yaki" domin su kawar da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.
Kazalika ECOWAS ta gargadi kasashen da ke goyon bayan Nijar da su shiga taitayinsu tana mai cewa za su gamu da fushinta idan ba su daddara ba. Da alama tana magana ne a kan Mali da Burkina Faso, wadanda suka goyi bayan sojojin na Nijar.
Tun da fari a bayaninsa na bude taron, Shugaba Tinubu ya ce “Mun fifita amfani da diflomasiyya wajen sasantawa a matsayin hanya mafi dacewa ta warware wannan takaddama".
Ya ce juyin mulkin da aka yi a makwabciyarsa Nijar yana da mummunan tasiri a kan gwamnatocin da aka zabe su bisa turbar dimokuradiyya a yankin.
"Taron yau ya bayar da muhimmiyar dama ta yin waiwaye da duba kan ci gaban da aka samu tun bayan taron da ya gabata.
"Yana da muhimmanci mu yi nazarin yadda kokarin da muke yi na shiga tsakani ke tasiri tare da gano duk wani kalubale da zai kawo tarnaki ga nasarar," ya ce.
Shugaba Tinubu ya ce dole ne su shigar da dukkan bangarorin da suka dace ciki har da jagororin juyin mulkin don fahimtar da su muhimmancin mayar da mulki ga Shugaba Bazoum.
Wakilan Majalisar Dinkin Duniya da na Kungiyar Tarayyar Afirka da kuma shugabannin kasashen Afirka ta Yamma ne suka halarci taron.